Iran Ta Hallaka Sojojin Amurka bayan Kai Masu Hare Hare Masu Zafi
- Iran ta kashe sojojin Amurka yayin da suke kare sansanin sojojin Amurka da na abokan hulɗa daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa
- Wani sojan Amurka ya ɓace, yayin da aka kwashe wasu huɗu zuwa asibiti domin samun magani
- Adadin sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin wanda aka fara a ranar 28, ga watan Fabrairun 2026 ya ƙaru zuwa 16
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Jordan - Iran ta kashe sojojin Amurka biyu a Jordan bayan ta kai wani harin makamai masu linzami kan sansanin da suke ciki.
An kashe sojojin ne yayin da suke kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai, a ranar Juma’a, 17 ga Yuli, 2026, yayin da wani soja na uku ya ɓace.

Source: Twitter
Rundunar sojojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM), ta sanar da hakan a ranar Asabar, 18 ga watan Yulin 2026 a shafinta na X.
Iran ta kashe sojojin Amurka
A cikin sanarwar, rundunar ta ce:
“A ranar 17 ga Yuli, an kashe sojojin Amurka biyu a Jordan yayin da United States Central Command (CENTCOM) da dakarun abokan hulɗa ke kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na Iran.”
“Bugu da ƙari, a halin yanzu wani soja ya ɓace ba a san inda yake ba.”
Wannan ne karon farko da aka kashe sojojin Amurka tun bayan da aka sake komawa faɗa makonni biyu da suka gabata. Lamarin ya sa adadin sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin ya kai 16.
An kai hari sansanin Amurka
A ranar Asabar, aƙalla makamai masu linzami biyu na Iran sun faɗa kan Muwaffaq Salti Air Base da ke Jordan, sansanin da ke karɓar sojojin Amurka da jiragen yaƙi.
Bidiyoyin da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta sun nuna lokacin da makaman biyu suka faɗa da kuma hayaƙi mai yawa da ya tashi a yankin nan take.
CENTCOM ta tabbatar da cewa an kashe sojojin Amurka biyu, yayin da wani na uku ya ɓace. An kuma kwashe wasu sojoji huɗu zuwa asibitoci domin samun magani.

Source: Twitter
Hare-haren Iran sun yi barna
Tashar Axios ta ce jami’an Amurka biyu sun ce hare-haren makamai masu linzami huɗu daban-daban da Iran ta kai sun sauka a sansanonin da sojojin Amurka ke ciki a Jordan cikin makon da ya gabata.
Wani jami’in Amurka ya ce an jikkata sojojin Amurka da dama a hare-haren, yayin da aka lalata jirage masu saukar ungulu da dama.
Jami’in ya kuma bayyana damuwa cewa hare-haren guda huɗu na nuna cewa Iran ta yi nasarar gano raunin da ke cikin tsarin kariyar Amurka a Jordan.
Amurka za ta sayar da makamai ga Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa ta amince da sayar wa Saudiyya makamai da kayan kariyar sama.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa darajar makaman da za a sayarwa Saudiyya ya kai kusan dala biliyan 1.96 domin inganta tsaronta.
Asali: Legit.ng

