Martanin da Kuwait, Bahrain Suka Yi Wa Iran da Ya Girgiza Birnin Tehran
- Kuwait ta ce dakarunta na sama sun dakile hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Iran
- Kasar Bahrain ta ce ta dakile tare da lalata wasu hare-haren sama da Iran ta kai mata
- Iran ta ce ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka biyu a Kuwait domin mayar da martani kan hare-haren Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Birnin Tehran, Iran - Kuwait da Bahrain sun ce dakarunsu na sama suna mayar da martani kan hare-haren Iran a ranar Lahadi, yayin da aka ji karar siren gargadi a kasashen biyu na Tekun Larabawa.
Sojojin Kuwait sun ce dakarun tsaronsu suna dakile hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuki na Iran.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton martanin kasashen biyu a ranar Lahadi, 19 ga watan Yulin 2026.
“Makaman tsaron sararin samaniyar Kuwait a halin yanzu suna fuskantar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na makiya, bayan mummunan harin zalunci da Iran ta kai,” sojojin kasar suka bayyana a cikin wata sanarwa.
Wani dan jaridar AFP ya ce an ji karar karaurawar gargadi a birnin Kuwait.
A Bahrain, inda rundunar sojin ruwa ta Amurka ta biyar (US Fifth Fleet) take da sansani, sojojin kasar sun ce dakarun tsaron sararin samaniyarsu sun “fuskanci, tare da dakile da lalata wasu munanan hare-haren sama” da Iran ta kai.
Wani dan jaridar AFP ya ce an ji karar fashewar abubuwa a Arewacin Bahrain, bayan da wani dan jaridar kamfanin ya ruwaito cewa an ji karar karaurawar gargadi a fadin babban birnin kasar, Manama.
Iran ta kai hari Kuwait
Da sanyin safiyar Lahadi, 19 ga watan Yulin 2026, sojojin Iran sun ce sun kai hari da jirage marasa matuka kan sansanonin sojin Amurka biyu da ke Kuwait domin mayar da martani kan hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Iran.
Iran ta ce a baya ta kaddamar da “manyan hare-hare da jirage marasa matuka masu kai harin kunar bakin wake” kan ma'ajiyar harsasai ta sojin Amurka da ke Camp Udairi da kuma tsarin radar Patriot da radar sa ido kan sararin samaniya da ke Ali Al Salem Air Base a Kuwait, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Iran ta ruwaito.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali: Girgizar kasa mai girma ta afku a Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Kuwait da Bahrain, wadanda ke karbar sansanonin sojin Amurka, sun fuskanci mafi yawan hare-haren da Iran ke kai wa makwabtanta na Tekun Larabawa tun bayan sake barkewar rikici a wannan watan, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Washington da Tehran.

Source: Getty Images
An kai hari kan cibiyoyin Kuwait
A ranar Asabar, Kuwait ta ce Iran ta kai hari kan wata cibiyar samar da wutar lantarki da ruwa da kuma wani wurin sarrafa man fetur, kafin Amurka ta sanar da kai hare-haren bama-bamai domin “hukunta” Iran kan mutuwar sojojin Amurka na farko tun bayan sake barkewar rikicin.
Rundunar Sojin Amurka ta yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta ce an kashe sojoji biyu a ranar Juma’a yayin da suke “kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami masu linzami na Iran da jirage marasa matuka."
Rundunar ta kuma ce har yanzu ana neman wani soja da ya bace a bakin daga.
Amurka ta kai hari kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Amurka sun ce sun kai sababbin hare-haren sama kan Iran domin “gaggawar hukunta” dakarun Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC).
An kai hare-haren ne bayan wani hari da Iran ta kai kan sansanin Amurka a Jordan ya kashe sojoji biyu, ya sa wani ya ɓace, yayin da aka kwashe wasu huɗu zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng
