Yaki Ya Yi Zafi: Amurka Ta Kai Sababbin Hare Hare kan Iran bayan Kashe Sojojinta
- Sojojin Amurka sun kai sabbin hare-haren sama kan Iran domin gaggawa hukunta dakarun rlundunar IRGC bayan an kashe sojojin Amurka biyu a Jordan
- Hare-haren sun kuma nufi rage ƙarfin Iran na barazana ga jigilar man fetur ta mashigar ruwa ta Hormuz
- Tun bayan fara yaƙin a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026 an kashe sojojin Amurka 16, yayin da sama da 430 suka jikkata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Iran - Sojojin Amurka sun ce sun kai sabbin hare-haren sama kan Iran domin “gaggawar hukunta” dakarun Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC).
An kai hare-haren ne bayan wani hari da Iran ta kai kan sansanin Amurka a Jordan ya kashe sojoji biyu, ya sa wani ya ɓace, yayin da aka kwashe wasu huɗu zuwa asibiti.

Source: Getty Images
Rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM), ta sanar da hakan ranar Asabar, 18 ga watan Yulin 2026 a shafinta na X.
CENTCOM ta an tsara hare-haren ne domin ƙara rage ƙarfin Iran na hana zirga-zirgar jiragen dakon man fetur ta mashigar ruwan Hormuz.
Kafin yaƙin, mashigar ruwan na samar da kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da ake samarwa a duniya. Sai dai Iran ta kusan rufe mashigar ga zirga-zirgar jiragen ruwa bayan fa yaƙin sakamakon hare-haren Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu.
Amurka ta bayyana dalilin hare-haren
CENTCOM ta ce:
“A yau da ƙarfe 6:00 na yamma agogon Gabashin Amurka, sojojin Amurka suka fara kai sababbin hare-haren sama kan Iran bisa umarnin babban kwamandan rundunar.”
“An tsara hare-haren ne domin ƙara rage ƙarfin Iran na barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci a mashigar ruwan Hormuz da kuma gaggawar hukunta dakarun Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran da suka kai hare-hare kan sojojin Amurka a Jordan a daren jiya.”
Sabbin hare-haren sun zo ne bayan sojojin Amurka sun sanar da mutuwar sojojinsu na farko sakamakon harin kai tsaye daga Iran tun kwanakin farko na sake barkewar yaƙin.
An kashe sojojin ne bayan harin jirgi mara matuƙi da makamai masu linzami da aka kai kan sansanin Amurka a Jordan a ranar Juma’a. Ba a bayyana sunayen sojojin da aka kashe ba, kuma CENTCOM ba ta ƙara fitar da wasu bayanai kan mutuwarsu ba.
Tashar Yahoo News ta ce tun bayan fara yaƙin, an kashe sojojin Amurka 16, yayin da sama da 430 suka jikkata.

Source: Twitter
Hare-haren sun shafi kudancin Iran
A cewar kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA, wanda ya ambato hukumomin yankin kudancin lardin Hormozgan, an kai hari kan wani yanki da ke kusa da Sirik, a mashigar ruwan Hormuz, da misalin ƙarfe 1:30 na dare agogon yankin.
A cikin wannan lardin, an kuma kai hari kan wani wuri da ke kusa da Hajiabad, yayin da aka ji fashe-fashe a Bandar Abbas.
Haka kuma, an kai hari kan wani yanki da ke kusa da tsibirin Qeshm, wanda ke cikin mashigar ruwan.
Iran ta jikkata sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu hare-haren da Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka a Jordan sun jikkata sojojin Amurka da dama.
An kai hare-haren ne kan aƙalla sansanonin soji biyu da ke Jordan, inda aka tabbatar da jikkatar wasu jami'an sojin Amurka bayan an kai wa cibiyoyinsu hari.
Asali: Legit.ng

