'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto bayan Fuskantar Turjiya wajen Jami'an Tsaro
- Akalla mutum 13 sun rasa rayukansu a hare-haren da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto
- Dakarun tsaro da 'yan sa-kai sun dakile yunƙurin mamaye Unguwan Lalle bayan fafatawar sa'o'i da dama
- Bayan sun gaza a Unguwan Lalle, maharan sun kashe mutum shida a Mazau, huɗu a Turtsawa da uku a Tsamaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Sokoto - Akalla mutum 13 sun mutu a sababbin hare-haren da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai kan ƙauyuka uku a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.
Hare-haren, da suka faru tsakanin yammacin ranar Alhamis da safiyar Juma'a, sun yi sanadin mutuwar mutum shida a ƙauyen Mazau, huɗu a Turtsawa ciki har da mata biyu, da kuma manoma uku a ƙauyen Tsamaye.

Kara karanta wannan
Rana ta baci: Ƴan bindiga sun yi arba da ƴan sanda bayan sun sace mutane a Sokoto

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton sababbin hare-haren da 'yan bindigan suka kai a ranar Juma'a, 17 ga watan Yulin 2026.
Dakarun tsaro sun dakile hari
Mazauna yankin sun ce da farko 'yan bindigar sun yi yunƙurin mamaye Unguwan Lalle a yammacin Alhamis, amma dakarun tsaro tare da 'yan sa-kai sun dakile harin bayan musayar wuta mai zafi da ta ɗauki sa'o'i da dama.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun janye ne bayan sun gamu da tsauraran matakan tsaro.
"Sojoji da 'yan sa-kai sun fafata da su na sa'o'i da dama. Mun yi amanna cewa 'yan bindigan sun yi asara mai yawa, amma sun kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu kamar yadda suka saba yi." In ji shi
Yadda hare-haren suka auku
Majiyar ta bayyana cewa bayan sun kasa mamaye Unguwan Lalle, 'yan bindigar sun nufi ƙauyen Mazau inda suka kashe mutum shida, sannan suka zarce Turtsawa inda suka kashe wasu huɗu, ciki har da mata biyu.
Ya ƙara da cewa saurin da jami'an tsaro suka ɗauka ya hana maharan ƙara kashe mutane.
A cewarsa, da safiyar Juma'a 'yan bindigar sun dawo suka yi wa manoman da ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki kwanton bauna a ƙauyen Tsamaye, inda suka kashe mutum uku.
"Sun sake yunƙurin kai mana hari lokacin da ake jana'izar waɗanda aka kashe da safiyar yau, amma sojojin da ke Unguwan Lalle sun isa cikin gaggawa suka kore su." In ji shi
Hare-haren sun ƙaru a Sabon Birni
Wani jagoran al'umma a Sabon Birni, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wannan na daga cikin jerin sabbin hare-haren da 'yan bindiga suka sake ƙaddamarwa a yankin.
Ya bayyana cewa tun ranar Laraba maharan sun yi garkuwa da manoma uku a Fadaman Sabon Birni.

Source: Twitter
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Ƙoƙarin jin ta bakin 'yan majalisar dokokin jihar Sokoto masu wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza da Hon. Sa'idu Ibrahim, bai yi nasara ba saboda ba su amsa kiran wayarsu ba.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa'i, ya ce har zuwa lokacin bai samu cikakken bayani kan harin ba.
"Har yanzu ban samu cikakken bayani game da hare-haren ba. Zan tuntuɓi jami'in 'yan sanda mai kula da yankin domin samun cikakkun bayanai."
- DSP Ahmad Rufai
'Yan bindiga sun sace darakta
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai wani mummunan hari a jihar Kebbi inda suka kashe wani mutum da kuma garkuwa da matarsa.
Maharan sun kashe Daraktan Ma'aikata na karamar hukumar Ngaski, Alhaji Nasiru Muhammed, bayan sun kai hari gidansa.
Asali: Legit.ng

