Manyan Labarai A Yau
Hakimin Dorayi a masarautar Kano, Alhaji Shehu Kabiru Bayero, ya yi bankwana da duniya a Masar, inda Masarautar Kano ta yi addu’ar Allah Ya ji kansa da rahama.
Yan adawar Isra’ila sun ce Benjamin Netanyahu bai cancanci ci gaba da zama firaminista ba bayan rahoton cewa UAE ta gargade shi kafin harin Hamas na 2023.
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tare ayarin Peter Obi a Benue, yana kira ga gwamnati ta gano tare da hukunta waɗanda suka haddasa lamarin.
Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban jam'iyyar ADC na jihar Edo, Kennedy Odion, inda suka sace kuɗi, motoci biyu da wasu kayayyaki masu daraja.
Lauyoyin APC a Osun sun musanta shigar da ƙara kan nasarar Ademola Adeleke, suna cewa jam’iyyar da ɗan takararta sun yanke shawarar ba za su ƙalubalanci zaɓen ba.
Kungiyar Middle Belt Forum ta goyi bayan Christopher Musa kan zargin Nasir El-Rufai da hannu a kisan Kudancin Kaduna, tana mai cewa tana da hujjoji.
Lauyoyin Nasir El-Rufai sun nemi N10bn daga Janar Christopher Musa kan zargin ɓata sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna da wasu kalaman da suka yi masa.
Matasa sun gudanar da zanga-zanga a Sokoto kan ci gaba da tsare malamin addini Dahiru Mai Barewa, lamarin da ya kai ga arangama da jami’an tsaro.
Adewole Adebayo ya ce ya san kura-kuran gwamnatin Bola Tinubu, amma ba zai zargi shugaban ƙasar ba idan ya gaje shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027
Manyan Labarai A Yau
Samu kari