An Zo Wajen: ICPC Ta Titsiye Gbajabiamila kan Badakalar Hukumar PFIPC

An Zo Wajen: ICPC Ta Titsiye Gbajabiamila kan Badakalar Hukumar PFIPC

  • Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta titsiye Femi Gbajabiamila kan zargin da ake yi game da PFIPC da ake takaddama a kai
  • Mai ikirarin shugabantar PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da karɓar N400m domin ya samu shugabancin hukumar
  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar ya musanta zarge-zargen tare da shigar da ƙarar N15bn kan Adeniyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffukan da Suka Shafi Hakan (ICPC) ta yi wa Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, tambayoyi kan rikicin da ya shafi hukumar PFIPC.

Adeniyi Adeyemi mai ikirarin shugabantar hukumar ya zargi Gbajabiamila da karɓar N400m domin ya taimaka masa wajen samun shugabancin hukumar mai cike da takaddama.

ICPC ta titsiye Gbajabiamila
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa lauyan Gbajabiamila ya tabbatar da cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya amsa gayyatar hukumar ICPC a ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Yadda aka cusa N1.3bn na ma'aikatar bogi a kasafin 2026

Adeniyi ya yi zargi kan Gbajabiamila

Adeniyi Adeyemi dai ya yi zargin cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya nemi kashi 48 na kudin fara aiki na N27.3bn da aka ware wa hukumar.

Hakazalika Adeyemi ya ce ya fara hulɗa da Gbajabiamila ne ta hannun Babatunde Tanimola, wanda yanzu ya rasu.

Ya kuma ce ya kamata a yi wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa tambayoyi game da mutuwar Tanimola mai cike da ce-ce-ku-ce.

Gbajabiamila ya musanta zarge-zarge

Sai dai Gbajabiamila ya musanta dukkan zarge-zargen, sannan ya shigar da ƙarar N15bn a kan Adeyemi.

A yayin da ake ta musayar zarge-zarge, Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC da ta binciki lamarin cikin kwanaki 30.

ICPC ta yi wa Gbajabiamila tambayoyi

Jiti Ogunye, lauyan Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa an yi wa wanda yake karewa tambayoyi, Premium Times ta kawo rahoton.

“Cikin cikakken haɗin gwiwa da ICPC, kamar yadda shugaban Najeriya ya bayar da umarni, ina tabbatar da cewa wanda nake karewa, Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar Najeriya, ya amsa gayyatar hukumar."

Kara karanta wannan

Mary Habila: Dalilin da ya sa iyayen budurwar da ta mutu a gidan Minista ba su so a binciki gawarta

"Kuma ya bayyana da misalin ƙarfe 3:00 na rana a ranar Litinin, 20 ga Yuli, 2026, a matsayin wani ɓangare na binciken da ake ci gaba da yi kan ayyukan hukumar ‘PFIPC’ ta bogi, da sauran batutuwa,” in ji shi.

Gbajabiamila ya amsa tambayoyi

Ogunye ya ce Gbajabiamila ya bayar da bayaninsa, ya amsa tambayoyin da aka yi masa yadda ya kamata, sannan ya koma bakin aikinsa.

“Wanda nake karewa ya bayar da bayaninsa, ya amsa tambayoyi yadda ya kamata, sannan ya koma bakin aikinsa." In ji shi
ICPC ta yi wa Gbajabiamila tambayoyi
Femi Gbajabiamila da Adeniyi Matthew Adeyemi Hoto: @femigbaja
Source: Twitter

Yadda PFIPC ta shiga kasafin kudin 2026

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi Matthew, ya bayyana yadda aka yi ta shiga cikin kasafin kudin shekarar 2026.

Adeniyi ya ce jami’an Ofishin Kasafin Kudi ne suka taimaka wajen shigar da hukumar cikin kasafin kudin gwamnatin tarayya bayan an kama shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng