EFCC na Daukar Ma'aikata a Boye? An jI Gaskiyar Zance

EFCC na Daukar Ma'aikata a Boye? An jI Gaskiyar Zance

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce labarin da ake yadawa cewa tana daukar ma’aikata a boye ba gaskiya ba ne
  • Hakazalika hukumar ta gargadi jama’a da su yi watsi da labarin tare da guje wa yada shi ga wadanda ba su san da shi ba
  • EFCC ta ce duk wata damar daukar ma’aikata tana sanar da ita ne ta kafafenta na sadarwa da aka tantance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta yi martani kan rahotannin cewa tana daukar ma'aikata a boye.

Hukumar EFCC ta karyata wani labari da ya yadu a kafafen sada zumunta cewa tana gudanar da daukar ma’aikata a boye, tana mai cewa labarin karya ne kuma yaudara ce.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

EFCC ta ce ba ta daukar ma'aikata
Shugaban hukumar EFCC na jawabi a wajen taro Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

EFCC ta musanta daukar ma'aikata

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X da aka tantance ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta gargadi jama’a da su guji yarda da labarin ko yada shi.

EFCC ta wallafa wani hoto mai dauke da kalmomin “Labaran karya” da kuma “Wannan labaran karya ne. Ku yi hattara!", inda ta yi watsi da jita-jitar daukar ma’aikata.

Abin da sakon karyar ya kunsa

Jaridar Leadership ta ce sakon da ya yadu ya yi ikirarin cewa:

“Ku tuntubi iyayen gidanku ooo. EFCC na daukar ma'aikata a sirrance.. Akwai yiwuwar za su fara zuwa wurin horarwa sati mai zuwa."

An kuma bukaci masu amfani da kafafen sada zumunta su aika da sakonnin sirri ba tare da bayyana sunayensu ba.

Da take mayar da martani kan ikirarin, hukumar EFCC ta shawarci ’yan Najeriya da su yi watsi da bayanin, tana jaddada cewa babu wani shirin daukar ma’aikata a boye da take gudanarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta garzaya kotu bayan kuskuren tura sama da N5m wani asusu

Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar damfarar daukar ma’aikata a intanet, inda masu damfara ke yawan amfani da tallan ayyukan bogi na EFCC wajen yaudarar masu neman aiki da karbar kudi daga jama’a ba tare da saninsu ba.

EFCC ta bayyana hanyar daukar ma’aikata

Hukumar ta sake jaddada cewa duk wani shirin daukar ma’aikata da take gudanarwa ana sanar da shi a hukumance ta kafafenta na sadarwa da aka tantance, kuma ba ta gudanar da irin wannan aiki a boye ko ta hannun wasu mutane.

Ta bukaci ’yan Najeriya da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani da ya shafi ayyukanta ta hanyar duba shafukanta da aka tantance kafin su dauki mataki ko su yada irin wannan sako.

EFCC ta ce ba ta daukar ma'aikata
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede a ofis Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta yi nasara kan Emefiele

A wani labarin kuma, Kotun Kolin Koli ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin ƙarshe na kwace da ke da alaka da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Kotun ta tabbatar da kwace filaye bakwai $2,045,000 da kuma takardun hannun jari da ake alakanta wa da Godwin Emefiele, tare da mayar da su mallakin gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng