"Mun bar Ka da Allah": Mazauna Sokoto Sun Tura Sako ga Gwamna kan Rashin Tsaro
- Wasu bayin Allah da aka raba da muhallansu a jihar Sokoto sun bayyana cewa ba za su yafewa gwamnatocin kasar nan da suka bari ana cin zarafinsu ba
- 'Yan bindiga sun tilasta mazauna Lalle da wasu ƙauyuka a Sabon Birni tserewa daga gidajensu saboda munanan hare-hare da ake kai wa ba dare ba rama
- Aƙalla ƙauyuka 15 sun koma kufai bayan hare-haren da aka kai a Tureta da Sabon Birni lamarin da ya sa mata, yara, mazajensu da dabbobi ke yin hijira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Mazauna garin Lalle da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto na ci gaba da tserewa daga gidajensu ba tare da sanin inda za su nufa ba.
Wannan na zuwa ne sakamakon yadda 'yan bindiga ke ci gaba da addabar al'ummar yankin. Harin na baya-bayan nan ya bar mutane da dama ba su da matsuguni, abinci ko kuma damar samun muhimman buƙatun rayuwa.

Source: Facebook
Rahotanni a jaridar The Guardian ta ruwaito cewa sun nuna cewa aƙalla ƙauyuka 15 sun zama kufai bayan hare-haren haɗin gwiwa da 'yan bindiga suka kai a ƙananan hukumomin Tureta da Sabon Birni na jihar Sokoto.
Jama'a sun tsere daga Sokoto
DNN ta wallafa bidiyo a shafinta na Facebook cewa hare-haren sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 52, yayin da daruruwan mutane suka rasa matsugunansu.
Lamarin ya ta'azzara matuƙa, inda mazauna yankin ke fama da rashin abinci, ruwa da kuma samun kulawar lafiya. Wasu daga cikin mutanen da suka tsere daga gidajensu.
Wasu daga cikinsu sun bayyana halin da suke ciki da cewa:
"Babu abin da za mu ce illa Allah Ya isa mana. Unguwar Lalle ta tashi gaba ɗaya. An ci amanarmu. Ga yunwa, ga rashin tsaro. Mun bar gwamnati da Allah. Mun bar ku da Allah."
Yan Sokoto sun aika sako ga gwamnati
Masu gudun hijirar sun kara da cewa sun fitar da rai da cewa gwamnati za ta taimaki rayuwarsu wajen hana yan bindiga kai masu hari.

Source: Original
Daya daga cikinsu ya ce:
"Duk sai Allah Ya isa mana. Ku kuna can kwance tare da yaranku, mu kuma muna ta gararamba da yaranmu. Gwamnatin jihar Sokoto ta cuce mu, ta yaudare mu. Ka duba, mu ma 'yan ƙasa ne a nan. An wulaƙanta mu a gwamnati, wallahi."
An kai hari jihar Sokoto
A baya, mun kawo labarin cewa ’yan kungiyar Lakurawa sun kai wani mummunan hari garin Girkau da ke karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Harin ya yi sanadin mutuwar jami’in dan sanda da fararen hula biyu, yayin da wasu suka samu raunuka Maharan sun kona motocin jami’an tsaro biyu tare da yin awon gaba da shanu masu yawa.
Mazauna yankin sun ce maharan dauke da makamai masu yawa sun afka garin tare da bude wuta kan jami’an tsaro da mazauna yankin. Hakan ya sa mutane da dama suka tsere domin neman mafaka.
Asali: Legit.ng

