Wata Sabuwa: Iran Ta Titsiye Jami'an Faransa 2 a Tehran, Faris Ta Yi Gargadi
- Gwamnatin kasar Faransa ta fusata biyo bayan zargin ci zarafin jami'anta biyu na diflomasiyya da ta ce jami'an tsaron Iran sun yi
- Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya bayyana cewa daya daga cikin jami'an an ci zarafinsa ta hanyar duka
- Lamarin ya faru ne a yayin da ake ci gaba da samun katsalandan da hare-haren makamai masu girma a yankin Gabas Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France – Gwamnatin ƙasar Faransa ta nuna fushinta game da abin da ta kira "mummunan matakin razanarwa" da jami'an tsaron ƙasar Iran suka ɗauka kan ma'aikatan jakadancinta guda biyu a Tehran.
Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya bayyana cewa jami'an tsaron Iran sun tsare jami'an diplomasiyyar ƙasar biyu na tsawon sa'o'i da dama, inda aka yi musu tambayoyi sannan aka ci zarafin ɗayansu ta hanyar duka.

Source: Getty Images
France24 ta ruwaito cewa Barrot ya bayyana damuwarsa matuka, yana mai cewa wannan mataki ya saɓa wa dokokin kare haƙƙin diplomasiyya na ƙasa da ƙasa.
Matakin da Faransa za ta ɗauka
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Barrot ya tabbatar da cewa an saki jami'an kuma suna lafiya a halin yanzu, inda ake sauran 'yan sa'o'i kalilan su koma gida Faransa.
Iran International ta wallafa cewa ya ce:
"Wannan farmaki abin takaici ne ƙwarai, musamman la'akari da cewa waɗannan jami'ai biyu su ne ke kula da shirye-shiryenmu na tallafa wa al'umma, musamman 'yan wasan kwaikwayo da masana kimiyya na Iran."
Barrot ya ƙara da cewa ya gargadi takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, cewa wannan mummunan al'amari ba zai wuce ba tare da an ɗauki mataki ba.
Haka zalika ya kuma jaddada cewa takunkumin Turai kan Iran zai ci gaba muddin ba ta dakatar da shirin nukiliyarta ba.

Source: Getty Images
Iran na kai hare-hare
A wani labarin kuma, rundunar dakarun tsaron juyin juya hali na Iran (IRGC) ta ikirarin kaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Bahrain da Kuwait.
Sanarwar da IRGC ta fitar ta bayyana cewa hare-haren na daga cikin jerin samame na "Nasr 2" domin daƙile sansanonin da Amurka ke amfani da su.
IRGC ta kuma ƙaryata kalaman shugaban Amurka, Donald Trump na cewa makamansu suna ƙarewa, tana mai cewa za su ci gaba da mai da martani muddin aka cigaba da rikicin.
Shugaban Faransa zai zo Najeriya
A wani labarin na daban, kun ji cewa jakadan ƙasar Faransa a Najeriya, Marc Fonbaustier, ya bayyana cewa shugaba Emmanuel Macron zai kai ziyarar aiki a Najeriya.
Fonbaustier ya bayyana wannan ne a lokacin bikinsu na ranar ƙasa a Abuja, shekaru biyu bayan ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai Faris.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an shirya ziyarar ne da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa kan kasuwanci, tsaro, da sauran fannoni.
Asali: Legit.ng

