Badakalar Biza: EFCC Ta Dauko Batun Bincikar Shugabar Hukumar NIS
- EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta yi magana kan binciken Shugabar Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, Kemi Nandap
- Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ana binciken wasu jami’an shige da fice kan zargin damfara da ta shafi biza
- EFCC ta ce binciken da ake gudanarwa na iya kai ga gurfanar da wasu jami’an hukumar NIS a gaban kotu saboda abubuwan da suka aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta karyata rahotannin da ke alakanta Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS), Kemi Nandap.
EFCC ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa ana bincikar Kemi Nandep kan zargin karbar kudade ba bisa ka’ida ba a harkar biza.

Source: Facebook
EFCC na gudanar da bincike
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ya fitar ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 a shafin X.
EFCC ta ce tana binciken zargin damfarar biza da ya shafi wasu jami’an shige da fice, amma babu wata alaka tsakanin shugabar hukumar da wadannan korafe-korafe.
Wannan bayani ya zo ne bayan rahotanni da kuma wasu maganganu a kafafen intanet da ke nuna cewa EFCC na binciken Nandap kan zargin karbar kudade ba bisa ka’ida ba a harkar biza.
“EFCC na sane da rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai game da zargin karbar kudade ba bisa ka’ida ba a harkar biza da ya shafi wasu jami’an Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, musamman wasu maganganu na boye da ke nuna cewa ana binciken Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice, Kemi Nandap."
“Hukumar na son bayyana babu wata shari’a ko bincike da ke tsakaninta da Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice,” in ji sanarwar
EFCC ta tabbatar da akwai kararraki
Sai dai EFCC ta tabbatar da cewa akwai shari’o’in laifuffukan da ake zargin wasu jami’an shige da fice da aikatawa da ke gaban Babbar Kotun Tarayya kan zargin damfarar biza.

Kara karanta wannan
Tura ta kai bango: Mutanen gari sun aika sako ga Tinubu kan hare haren 'yan bindiga
A cewar hukumar, ana ci gaba da bincike kuma hakan na iya kai ga gurfanar da wasu jami’an shige da fice.
“Akwai kararraki da ake ci gaba da yi kan wasu jami’an shige da fice a Babbar Kotun Tarayya bisa zargin damfarar biza."
“Ana ci gaba da gudanar da karin bincike, kuma akwai yiwuwar a gurfanar da wasu jami’an NIS saboda zargin aikata damfara nan gaba kadan."
“Duk da haka, Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ba ta da wata alaka ko kadan da wadannan bincike,” in ji sanarwar
Hukumar ta bukaci ‘yan jarida da kafafen yada labarai su rika tuntubar ta domin tabbatar da bayanai kafin wallafa su, don kauce wa karkatar da bayanai game da ayyukanta.

Source: Facebook
An alakanta EFCC da bincikar Nandep
The Punch ta ce wannan bayani ya biyo bayan zargin alakanta wasu manyan jami’an Hukumar Shige da Fice da wani bincike da EFCC ke gudanarwa kan zargin wani tsarin karbar kudade ba bisa ka’ida ba daga baki da suka wuce wa’adin bizar su.
An yi zargin cewa wasu jami’an shige da fice sun karbi kudade ba bisa ka’ida ba daga baki da suka wuce wa’adin bizar su maimakon aiwatar da hukuncin da Dokar Biza ta Najeriya ta 2025 ta tanada, wadda ta wajabta biyan tarar dala $15 a kowace rana ga dan kasar waje da ya ci gaba da zama a Najeriya bayan karewar bizar sa.
EFCC ta musanta daukar ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta yi martani kan batun cewa tana daukar sababbin ma'aikata a boye.
Hukumar EFCC ta karyata labarin daukar ma'aikatan a boye wanda ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ta ce karya ce tsagwaronta.
Asali: Legit.ng

