A Karon Farko Messi Ya Yi Magana bayan Rashin Nasarar Argentina a hannun Spain
- Lionel Messi ya ce ciwon rashin nasarar da suka yi a wasan karshe a gasar cin kofin duniya zai yi wuya ya warke
- Spain ta doke Argentina da ci 1-0 bayan an yi karin lokaci, inda ta lashe kofin duniya karo na biyu a tarihinta
- Argentina ta zama kasa ta farko tun Brazil a 1998 da ta kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya sau biyu a jere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
New York, Amurka – Kyaftin din Argentina, Lionel Messi, ya yi magana a karon farko bayan tawagarsa ta sha kashi a hannun Spain a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 a Amurka.
Dan wasan gaba na Inter Miami FC ya amince cewa zai yi wuya a shawo kan wannan rashin nasara, amma ya bayyana alfahari da irin nasarar da tawagarsa ta samu.

Kara karanta wannan
Miliyoyin dalolin da Sifen da sauran kasashe 48 suka samu a gasar cin kofin duniya

Source: Instagram
Messi, wanda bai yi magana da manema labarai ba bayan wasan karshe da aka buga ranar Lahadi a New York, ya wallafa sakonsa na farko a shafinsa na Instagram ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 bayan Argentina ta sha kashi da ci 1-0 a karin lokaci.
Kasar Spain ta lashe kofin duniya
Spain ta lashe kofin duniya karo na biyu bayan Ferran Torres ya zura kwallon da ta ba ta nasara a karin lokaci.
Argentina ta sha fama wajen samar da damarmaki masu kyau a wasan, inda har zuwa minti na 117 ne ta samu hari na farko da ya nufi raga.
Wace magana Lionel Messi ya yi?
Da yake mayar da martani kan rashin nasarar, Messi ya bayyana cewa radadin rashin lashe wasan karshe yana da matukar girma, amma ya ce zai ci gaba da daraja tafiyar da ta kai Argentina wasan karshe na gasar cin kofin duniya a karo na biyu a jere.
“Radadin yana da girma sosai, kuma zai yi wuya a gare ni na warkar da wannan rauni. Amma zan kuma rike dukkan abubuwan alheri... Tare da wasannin da muka nuna bajinta a filin wasa, kuma hakan zai kasance har abada a cikin tunaninmu, tare da goyon bayan daukacin kasa wanda, tare da aiki da kokarin wannan kungiya, ya kai mu sake kasancewa cikin mafiya kyau a duniya."
- Lionel Messi
Dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas ya yabawa abokan wasansa saboda kai wa wasan karshe na gasar cin kofin duniya sau biyu a jere, duk da cewa sun kasa kare kofin da suka lashe a Qatar shekaru hudu da suka gabata.
“Yau yana da wuya a tantance abin da muka cimma, amma wannan kungiya ta kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya sau biyu a jere.”
- Lionel Messi
Messi ya gode wa ’yan Argentina
Messi ya kuma gode wa ’yan Argentina saboda irin goyon bayan da suka ci gaba da ba tawagar a duk tsawon gasar.
“Na gode kwarai da gaske daga zuciya ta saboda kowanne gaisuwa da kowanne sako. Har yanzu mun samu damar hada kan kasa baki daya, muna kasancewa tare tare da raba babban alfaharin kasancewa ’yan Argentina.”
- Lionel Messi
Dan wasan mai shekaru 39 ya kammala sakonsa da taya Spain murnar nasarar da ta samu.
“Ina kuma son taya Spain murnar lashe gasar,” in ji shi.

Source: Getty Images
Jaridar The Punch ta ce Argentina ta shiga gasar ne a matsayin zakarar da ke kare kambunta bayan ta lashe kofin a Qatar a shekarar 2022.
Ko da yake ta kasa kare kambunta, tawagar Lionel Scaloni ta zama ta farko tun Brazil a shekarar 1998 da ta kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta maza sau biyu a jere.
Mbappe ya zarce Lionel Messi
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan wasan gaba na kasar Faransa, Kylian Mbappe ya zarce Lionel Messi a gasar cin kofin duniya.
Kylian Mbappe ya zama dan wasan da ya fi kowa yawan zura kwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya, inda yake da kwallaye 21.
Asali: Legit.ng

