Jigawa, Filato da wasu jihohi 6 da suka samu sababbin kwamishinonin 'yan sanda

Jigawa, Filato da wasu jihohi 6 da suka samu sababbin kwamishinonin 'yan sanda

  • Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya amince da sauya Kwamishinonin 'Yan Sanda a jihohi takwas da wasu manyan sassan rundunar
  • Sauyin ya biyo bayan amincewar Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan Sanda, domin ƙara inganta shugabanci da ayyukan tsaro
  • Sababbin Kwamishinonin 'Yan Sanda za su jagoranci jihohi da muhimman sassan rundunar domin ƙarfafa aikin leƙen asiri da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin wasanni, siyasa da al'amuran yau da kullum, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

FCT, Abuja - Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Disu, ya amince da tura sababbin Kwamishinonin 'Yan Sanda zuwa rundunonin jihohi takwas da kuma wasu muhimman sassan rundunar 'yan sanda a faɗin ƙasar.

Sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar ta bayyana cewa an yi sauyin ne bayan amincewar Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan Sanda.

Kara karanta wannan

An gano kasashe 3 da gwamnatin Tinubu ta yi nazarinsu don kafa ƴan sandan jihohi

An nada sababbin kwamishinonin 'yan sanda
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

CSP Ani Iniedu ya sanya sanarwar ne a shafin Facebook na rundunar 'yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026.

Sanarwar ta ce matakin na da nufin ƙarfafa ingancin ayyukan rundunar, inganta shugabanci a rundunonin jihohi da kuma ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake yi a harkokin aikin 'yan sanda.

Jihohin da aka tura sabbin kwamishinoni

Sanarwar ta bayyana cewa sababbin Kwamishinonin 'Yan Sanda da aka tura jihohi sun haɗa da:

  • Afolabi Wilfred Olutokunbo – Jihar Abia
  • Ayodeji Faniyan – Jihar Plateau
  • Saka Adewale Ajao – Jihar Bayelsa
  • Ajo Geoffrey Ordue – Jihar Cross River
  • Nanna Oji Ama – Jihar Anambra
  • Patrick Daaor – Jihar Edo
  • Tani Murtala – Jihar Jigawa
  • Samuel Erale – Jihar Delta

An tura wasu zuwa muhimman sassan rundunar

Sufeto Janar ya kuma amince da tura wasu Kwamishinonin 'Yan Sanda zuwa muhimman sassan rundunar da suka haɗa da Sashen Leƙen Asiri na Rundunar (Force Intelligence Department), Sashen Binciken Manyan Laifuka (Force Criminal Investigation Department), Sashen Kuɗi da Gudanarwa, Sashen Horo da Ci Gaba, Kwalejin 'Yan Sanda da kuma Police Staff College.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun yaba wa Tinubu duk da matsalolin tsaro da ake ciki

Sanarwar ta ce sauran waɗanda aka tura sun haɗa da:

  • CP Yemi John Oyeniyi – Sashen Leƙen Asiri da Horo, Force Intelligence Department (FID), Abuja.
  • CP Charles Ezekwesiri Dikee - Sashen INTERPOL na Force Criminal Investigation Department (FCID), Abuja.
  • CP Aina Adesola – Sashen Kuɗi da Gudanarwa (DFA) da Sashen Horo da Ci Gaba (DTD), Hedikwatar Rundunar (FHQ), Abuja.
  • CP Uduak Ita Otu – Sashen Yaƙi da Safarar Mutane (AHT), FCID Annex, Alagbon, Legas.
  • CP Abdullateef Ajape Yusuf – Babban Sashen Bincike (General Investigation), FCID, Abuja.
  • CP Taiwo A. Adedeji – Rundunar Yaƙi da Ta'addanci (CTU), Hedikwatar Rundunar, Abuja.
  • CP Ajayi Oluyemi – Sashen Yaƙi da Safarar Mutane (AHT), FCID, Abuja.
  • CP Bolanle Aremu – Sashen Kuɗi da Gudanarwa (DFA), Hedikwatar Rundunar, Abuja.
  • CP Ibrahim Lukunche Usman – Sashen Bincike na DTD, Hedikwatar Rundunar, Abuja.
  • CP Mohammed Hassan Ahmed – Mataimakin Kwamandan Police Staff College, Jos.
  • CP Rita Oyintare Oki – Sashen Gudanarwa na FCID Annex, Kaduna.
  • CP Ibrahim Umar D. Zungura – sabon muƙami kamar yadda sanarwar ta tanada.

Kara karanta wannan

Akwai ladar N60m: Sojoji sun saki hotuna da bayanan 'yan ta'adda 2 da ake nema

An yi sababbin kwamishinonin 'yan sanda
Olatunji Disu na gabatar da jawabi Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Sauran jami'an da sauyin ya shafa

Sanarwar ta kuma bayyana cewa:

  • An tura CP Nelson Nwamana zuwa Police Academy da ke Kano.
  • An naɗa CP Mohammed Hassan Ahmed a matsayin Mataimakin Kwamandan Police Staff College da ke Jos.
  • An tura CP Rita Oyintare Oki zuwa Sashen Kuɗi da Gudanarwa na Hedikwatar Rundunar da ke Legas.
  • An tura CP Danbaba Mohammed Labbo zuwa FCID Annex da ke Gombe.

Sharuddan VeryDarkMan ga 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa VeryDarkMan ya bayyana sharuddan da ya ce dole ne a cika kafin ya amsa gayyatar rundunar 'yan sandan Najeriya.

VeryDarkMan ya ce a shirye yake ya bayyana gaban masu bincike, amma ya dage cewa dole ne a gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci domin jama'a su gamsu da tsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com