Dara Ta Ci Gida; 'Yan Sanda Sun Yi Wa Shugaban Hukumar ICPC Kwace Kudi

Dara Ta Ci Gida; 'Yan Sanda Sun Yi Wa Shugaban Hukumar ICPC Kwace Kudi

  • Jami’an ’yan sanda huɗu sun shiga hannu a Abuja bisa zargin karɓar N53,000 daga Shugaban ICPC, Dr Musa Aliyu (SAN)
  • Kwamishinan ’yan sandan Abuja ya ce jami’an sun kafa shingen bincike ba bisa ƙa’ida ba a yankin Banex na Wuse
  • Ya ce an kama jami’an ne bayan bincike ya gano cewa sun bar wuraren aikinsu suka kafa wurin karɓar kuɗi daga masu ababen hawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta tsare jami’an ’yan sanda huɗu bisa zargin karɓar N53,000 daga Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC), Dr Musa Aliyu (SAN).

'Yan sandan sun karbi kudaden ne a lokacin da suka tsayar da shi ba bisa ƙa’ida ba domin bincike a Abuja.

'Yan sanda sun tatsi kudi a hannun shugaban ICPC
Shugaban hukumar ICPC, Abduljalal Musa Aliyu Hoto: ICPC Nigeria
Source: Facebook

Kwamishinan ’yan sandan FCT, Ahmed Sanusi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 yayin da yake yi wa ’yan jarida jawabi a Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Abin da Trump ya ce bayan Iran ta kashe sojojin Amurka

Yadda aka tatsi shugaban ICPC

Ahmed Sanusi ya bayyana jami’an a matsayin “barayi” waɗanda bai kamata su sanya kayan ’yan sanda ba, rahoton PM News ya tabbatar da hakan.

Ya ce jami’an sun kafa shingen bincike ba bisa izini ba a kusa da yankin Banex na Wuse bayan sun bar wuraren da aka tura su aiki, inda suka karɓi kuɗin daga shugaban ICPC ba tare da sanin matsayinsa ba.

A cewarsa, jami’an sun tilasta wa shugaban ICPC cire N53,000 ta hannun wani mai POS, inda ya biya kuɗin cirar kudin kafin jami’an su raba kuɗin a tsakaninsu.

“Dole na faɗi a nan cewa a yanzu haka muna tsare da ’yan sanda kusan huɗu waɗanda suka yi nasarar karɓar kuɗi daga wani babban mutum ba tare da sanin cewa shi mutum ne mai muhimmin matsayi a cikin al’umma ba. A taƙaice, sun karɓi kuɗi daga Shugaban ICPC.
“Sun karɓi N53,000 daga gare shi. Sun kai shi wajen wani mai POS, ya cire kuɗin, ya biya kuɗin caji, sannan suka raba kuɗin a tsakaninsu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Bincike ya gano gurbatattun 'yan sanda

Kwamishinan ya ce bincike ya gano cewa jami’an sun bar wuraren da aka tura su aiki, sannan suka kafa ƙungiyar masu laifi da ta kafa shingen bincike ba bisa ƙa’ida ba domin karɓar kuɗi daga masu ababen hawa.

“Ƙungiya ce ta masu laifi waɗanda suka bar sassa daban-daban, suka haɗu, suka koma Wuse Banex, suka kafa shingen bincike inda suka aikata wannan laifi kafin su tsere,” in ji shi.

Ya ce rundunar ta ayyana jami’an a matsayin waɗanda ake nema kafin ta kama shugaban ƙungiyar, wanda bayanan da ya bayar suka taimaka wajen kama sauran mambobin ƙungiyar.

“Mun kama su duka. Za mu tabbatar an hukunta su sosai. Waɗanda ya kamata a sallama daga aikin ’yan sanda kuwa, tabbas za a sallame su." In ji shi
An cafke 'yan sanda a Abuja
Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Ahmed Sanusi Hoto: @FCT_PoliceNG
Source: Twitter

ICPC ta maka likitan El-Rufai a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar ICPC ta shigar da karar likitan Nasir Ahmad El-Rufai, Bello Abubakar a kotu bayan tsare shi da aka yi.

ICPC ta yi zargin cewa Farfesa Bello Abubakar ya nemi ya yaudari hukuma, a ba Malam El-Rufai beli da sunan yana fam da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng