'Kowa na Tsoron Mutuwa,' An fara Tursasa Mutane Shiga Aikin Soja a Kasar Ukraine
- Wani tsohon soja ya ce an yi masa mummunan duka yayin da yake taimakawa jami’an daukar sababbin sojoji cafke masu guje wa shiga soja
- Rahotanni sun nuna hare-hare kan jami’an daukar sojoji na karuwa, yayin da gwamnati ke fama da matsalar samun sababbin mayaƙa a fagen daga
- Masana sun ce tsoron mutuwa, yaki mai tsawo da kuma tsauraran hanyoyin daukar sojoji ne suka haddasa karuwar tashin hankali a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Ukraine - Vasyl Krupych, wani tsohon soja yana da cikakkiyar masaniyar yadda sojoji ke fafata yaki domin kare Ukraine, kuma ya bada labarin abin da ya faru.
Ya ce ya tsallake rijiya da baya a yakin gabashin yankin Donbas, inda ya fuskanci hare-haren sojojin Rasha a lokuta da dama. A cewarsa, wani lokaci addu’a kawai yake yi, wani lokaci kuma hawaye ke zuba masa yayin da yake kokarin tsira.

Source: Getty Images
Yadda ake tilasta wa mutane shiga aikin soja
Sai dai a watan Disamban bara, bayan an mayar da shi aiki a bayan fage, ya ce wasu ’yan kasarsa ne suka kai masa hari yayin da yake taimakawa jami’an daukar sabbin sojoji wajen neman mutanen da ke guje wa shiga aikin soja, in ji rahoton BBC.
A cewarsa, wasu maza biyu sun ki nuna takardunsu sannan suka tsere. Yayin da jami’an suka bi su, an kai masa hari da sandar ƙarfe.
Ya shafe makonni shida a asibiti yana jinya.
"Sun karya min haƙarƙari, na kasa numfashi lokacin da nake kwance," in ji Krupych.
Ya ce abin da ya fi ba shi ciwo shi ne yadda ake kai wa sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu hari daga mutanen da suke karewa.
Hare-hare kan jami’an daukar sojoji na karuwa
Jami’ar da ke kula da kare haƙƙin sojojin Ukraine ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun zama ruwan dare.
Ta ce matsalar na ƙara muni yayin da ƙasar ke fama da ƙalubalen samun sabbin mayaƙa a shekara ta biyar da fara mamayar da Rasha ta yi.
Sabon rahoton rundunar ’yan sandan ƙasar ya nuna cewa an samu fiye da hare-hare 600 kan jami’an daukar sojoji zuwa yanzu.
A watan Afrilu ne aka fara samun manyan hare-hare bayan da aka kai wa wasu jami’an hari da wukake, inda ɗaya ya mutu.
A wannan watan kuma, mutane kusan 200 sun kewaye jami’an daukar sojoji a birnin Lviv tare da lalata motarsu yayin da suke ƙoƙarin cafke wani da ake zargin ya guje wa shiga soja.
Lamarin ya jawo hankalin shugaban ƙasar Volodymyr Zelensky, wanda ya yi Allah wadai da kai hari kan jami’an soja.

Source: Getty Images
Dalilin fushin jama'a
Masu nazari sun ce akwai dalilai da dama da suka haddasa wannan yanayi, kamar yadda rahoton Yahoo News ya nuna.
Wasu mutane na tsoron komawa fagen daga saboda kusan kowa ya san wani da aka kashe ko aka jikkata. Sauran kuma sun gaji da yakin da ba a ga ƙarshensa ba.

Kara karanta wannan
An koma gidan jiya; ‘yan kasuwan da suka shigo da mai sun yi kara kudin fetur daga N1200
Dan majalisar adawa Oleksandr Honcharenko ya ce gwamnati ta fara amfani da hanyoyin da suka yi tsauri wajen daukar sabbin sojoji.
Ya ce jami’ai na bibiyar mutane a kan tituna, kuma wani lokaci ana amfani da ƙarfi wajen kama su.
A cewarsa, amfani da tashin hankali wajen daukar mutane ne ya haddasa mayar da martani da tashin hankali daga jama'a.
Sojojin Ukraine sun kashe 'yan Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, ana cigaba da samun bayanai game da 'yan Najeriya da suka rasu bayan shiga soja a yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine.
Gwamnatin Ukraine ta fitar da sunayen wasu 'yan Najeriya da ta bayyana cewa ta ragargaje su sun mutu bayan wani farmaki da ta kai musu.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan jakadan Rasha a Najeriya ya fito karara ya karyata rahoton da ke cewa suna daukar 'yan kasar nan.
Asali: Legit.ng

