Zaben 2027: Kwankwaso Ya Bayyana Yarjejeniyar da Ke Tsakaninsa da Peter Obi
- Rabiu Kwankwaso ya ce ya yi amanna cewa Peter Obi zai cika alkawarin yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a 2027
- Ya bayyana cewa shi da Obi sun sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tanadi komawar mulki Arewa bayan wa’adin shekaru huɗu
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce yarjejeniyar ta shafi jam’iyyar da kuma wata yarjejeniya ta daban tsakaninsa da Obi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi magana kan yarjejeniyar da ke tsakaninsa da Peter Obi.
Kwankwaso ya ce ya yi amanna cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, zai cika alkawarin yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a 2027.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels Tv da aka watsa ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan
A karshe, Peter Obi ya bar boye boye, ya fadi dalilin daukar Kwankwaso mataimakinsa
Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce an sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tanadi cewa mulki zai koma Arewa bayan wa’adi ɗaya na shekaru huɗu.
Kwankwaso ya yarda da alkawarin Obi
Da aka tambaye shi ko alkawarin Obi na yin wa’adi ɗaya ne kawai ya kasance “tabbatacce”, Kwankwaso ya ce ba shi da dalilin shakkar tsohon gwamnan na jihar Anambra.
“Eh, ni da kaina na yarda da shi kuma… ban yi tunanin cewa, bisa abin da na sani game da shi yanzu… zai sauya ra’ayinsa idan lokaci ya yi ba. Mu duka mutane ne masu mutunci, duk da cewa mun amince mu rubuta yarjejeniyar a takarda,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko an rubuta yarjejeniyar a takarda, Kwankwaso ya ce jam’iyyar ta sanya hannu kan wata yarjejeniya, yayin da shi da Obi kuma suka sanya hannu kan wata yarjejeniya ta daban.
“Mun yi wata yarjejeniya a madadin jam’iyyar, sannan mun yi wata yarjejeniya tsakanin mu biyun,” in ji shi.
Yarjejeniyar za ta mayar da mulki Arewa
Kwankwaso ya bayyana cewa yarjejeniyar ta tanadi cewa bayan wa’adin shekaru huɗu, za su ci gaba da aiki tare a matsayin ƙungiya, jam’iyya, abokai da ’yan’uwa.
“Yarjejeniyar ita ce abin da ka faɗa, cewa bayan shekaru huɗu… za mu yi aiki tare, mu kasance ƙungiya ɗaya, a matsayin jam’iyya, abokai, ’yan’uwa da makamantansu… ta yadda bayan wa’adinsa, ko wa’adinmu, na shekaru huɗu, daga 2027 zuwa 2031, mulki zai koma Arewa, kuma wannan ita ce babbar yarjejeniyar,” in ji shi.
Meyasa Kwankwaso ya amince da Obi?
Da yake bayyana dalilin da ya sa ya amince da matsayin mataimakin shugaban ƙasa duk da cewa a baya yana neman kujerar shugaban ƙasa, Kwankwaso ya ce yanayin siyasar yanzu ya dace da shugaban ƙasa daga Kudu na wa’adin shekaru huɗu kafin mulki ya koma Arewa.
“Mun ji tare cewa ya kamata shugabancin ƙasa ya koma Kudu na shekaru huɗu, sannan bayan haka ya koma Arewa. Mun yi amanna cewa wannan ya kamata ya zama matsayar kowa a wannan ƙasa domin mu ci gaba tare a matsayin yan'uwa, Arewa da Kudu,” in ji shi.

Source: Facebook
Dalilin Peter Obi na daukar Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya bayyana dalilin zabar Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.
Peter Obi ya bayyana cewa ya zaɓi Rabiu Kwankwaso ne saboda suna da manufa iri ɗaya ta yaƙi da talauci ta hanyar ilimi da bunƙasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng
