'Ba Zan Yi Rashin Nasara ba a Zaben 2027'; Peter Obi Ya Kawo Dalili

'Ba Zan Yi Rashin Nasara ba a Zaben 2027'; Peter Obi Ya Kawo Dalili

  • Peter Obi mai neman mulkin Najeriya ya bayyana cewa ya na da yakinin zai yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Ɗan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NDC ya ce zaɓen ba ya tsakaninsa da gwamnati, sai dai tsakanin al’umma da gwamnatin Najeriya
  • Tsohon gwamnan na Anambra ya ce shi wani makami ne kawai da ‘yan Najeriya ke amfani da shi wajen neman sauyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa ya na da yakinin zai yi nasara.

Peter Obi ya bayyana cewa zaɓen ba fafatawa ce ta siyasa tsakaninsa da gwamnati mai ci ba, illa dai tsakanin ‘yan Najeriya da gwamnatin ƙasar.

Peter Obi ya ce zai yi nasara a 2027
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce Peter Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka wallafa a cikin wani bidiyo da ya yaɗu sosai a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya haramta zabe kwata kwata, zai cigaba da mulki a Nicaragua

Meyasa Peter Obi ba zai fadi ba?

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce ya ɗauki kansa a matsayin wakilin ‘yan Najeriya da ke neman sauyi, yana mai jaddada cewa al’umma ce za ta tantance sakamakon zaɓen.

“Ba zan sha kaye ba saboda yanzu zaɓen ya koma tsakanin al’umma da gwamnatin Najeriya. Na yi imanin cewa mutane sun sha wahala sosai,” in ji Obi

Peter Obi ya ƙara da cewa bai kamata a ɗauki zaɓen a matsayin fafatawar da ta shafi kansa kai tsaye ba.

“Wannan zaɓen ba wai ni ne zan gaya wa mutane abin da za su yi ba, domin al’umma ce za ta yi nasara ko ta sha kaye a kan gwamnati. Don haka, duk abin da suka yanke shawarar yi, ban sani ba saboda ba ni ne nake iko da su ba. Ko da za su je kotu, al’umma ce za ta kai gwamnati ƙara. Saboda haka, wannan zaɓen yana tsakanin al’umma da gwamnati.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya bayyana yarjejeniyar da ke tsakaninsa da Peter Obi

Peter ya ce zabe ne tsakanin gwamnati da jama'a

Peter Obi ya bayyana cewa shi kawai wani makami ne da ‘yan Najeriya ke amfani da shi wajen cimma burinsu, rahoton Daily Post ya nuna hakan.

“Ni kawai ana amfani da ni ne a matsayin kayan aiki don tsayawa a madadin al’umma. Idan na yi nasara, abu ɗaya da dole ne na dawo da shi shi ne tabbatar da bin doka da oda; dole ne mu samu bin doka da oda,” in ji shi
Obi zai yi nasara a zaben 2027
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Yarjejeniyar Kwankwaso da Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwaasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi magana kan yarjejeniyar da ke tsakaninsa da Peter Obi.

Kwankwaso ya ce ya yi amanna cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, zai cika alkawarin yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a 2027.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce an sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tanadi cewa mulki zai koma Arewa bayan wa’adi ɗaya na shekaru huɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng