An Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Ta'addan ISWAP Suka Farmaki Sansanin Sojoji

An Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Ta'addan ISWAP Suka Farmaki Sansanin Sojoji

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da ake zargin mayakan ISWAP ne suka kai wa sansanin sojoji da ke Gajigana a jihar Borno
  • Mayakan sun kai harin da babura da motoci masu ɗauke da bindiga, amma sojoji sun tilasta musu ja da baya cikin rudani
  • Sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga, yayin da aka yi wa wata motar yaƙi ƙananan lahani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da ake zargin mayakan ISWAP ne suka kai wa sansanin Forward Operating Base (FOB) a jihar Borno.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a sansanin da ke Gajigana, ƙaramar hukumar Nganzai a jihar Borno, inda sojoji suka yi wa maharan mummunar barna.

Sojoji sun fafata da 'yan ISWAP
Dakarun sojoji a fagen fama Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tirkashi: 'Yan ta'addan ISWAP sun sake yunkurin sace dalibai a makaranta

'Yan ISWAP sun kai hari sansanin sojoji

Majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:20 na yammacin ranar Lahadi, 19 ga Yuli, lokacin da ɗumbin ’yan ta’addan suka nufi sansanin sojojin a kan babura da dama, tare da goyon bayan motoci biyu masu ɗauke da manyan bindigogi, yayin da wasu mayakan suka taho a ƙafa.

Majiyoyin sun ce sojojin Bataliya ta 212 sun gano maharan tun da wuri, sannan suka buɗe musu wuta mai ƙarfi, lamarin da ya dakile harin tare da tilasta wa maharan tserewa cikin rudani.

An yi musayar wuta

Jim kaɗan bayan fara musayar wuta, tawagar ƙarin sojoji ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Bataliya ta 212 ta isa wurin domin ƙarfafa sansanin da kuma daidaita lamarin.

A cewar majiyoyin, maharan sun yi asara mai yawa yayin harin da bai yi nasara ba, inda aka ruwaito cewa wasu daga cikin abokan aikinsu da suka tsere sun ja gawawwakin mayakan da suka mutu.

Kara karanta wannan

Iran ta hallaka sojojin Amurka bayan kai masu hare hare masu zafi

Sojoji sun fatattaki 'yan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

Sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga yayin artabun, amma an kula da su kafin a kwashe su zuwa asibiti domin ci gaba da ba su magani.

Sojojin sun kuma samu ƙananan lahani ga kayan yaƙinsu, bayan makamin roka (RPG) ya lalata jikin wata motar yaƙi da tayoyinta huɗu yayin musayar wutar.

Majiyoyin soji sun ce za a gudanar da bincike a fagen daga domin tantance cikakkiyar asarar da maharan suka yi tare da kwato duk wani makami ko kayan aiki da suka bari a baya.

Sojoji sun ceto dalibai a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun dakile yunƙurin sace ɗalibai da dama da ake zargin ƴan ta’addan ISWAP ne suka kai a jihar Borno.

Sojojin sun gwabza da 'yan ta'addan ne bayan sun kai hari a makarantar Federal Government Girls College (FGGC), inda suka ceto ɗalibai 46.

Wasu sassan gine-ginen makarantar sun lalace yayin arangamar, amma sojoji tare da jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun yi nasarar shawo kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng