"Ya Mutu Yana Kaina": Sababbin Bayanai Sun Fito kan Mutuwar Abacha
- Tsohon mataimakin daraktan DSS ya ce Sani Abacha ya rasu da misalin ƙarfe 4:05 na asuba yayin da yake tare da wata ma’aikaciyar lafiya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Dennis Amachree ya ce matar ta tsere zuwa Legas bayan ta gano cewa Abacha ya daina motsi bayan sun kadaita a cikin daki
- Tsohon jami'in na DSS ya ce bayanin matar ya karyata ra’ayoyin makirci da suka dabaibaye mutuwar tsohon shugaban ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dennis Amachree, tsohon mataimakin daraktan Hukumar DSS, ya bayyana yadda ya ce Sani Abacha, tsohon shugaban ƙasar Najeriya, ya yi bankwana da duniya a lokutan ƙarshe na rayuwarsa.
Abacha ya mulki Najeriya a matsayin shugaban mulkin soja daga Nuwamba 1993 zuwa Yuni 1998, yayin da mutuwarsa ta ci gaba da kasancewa cikin ce-ce-ku-ce da ra’ayoyin makirci.

Source: Getty Images
Bayanin Amachree kan mutuwar Abacha
A cewar The Nation, Amachree ya bayyana nasa bayanin kan lokutan ƙarshe na Abacha a cikin sabon littafinsa mai suna DSS @40: My Journey Behind the Shield.
Amachree, wanda a lokacin mutuwar Abacha yake mataimakin daraktan ayyuka da leƙen asiri a ofishin DSS na Legas, ya ce tsohon shugaban mulkin sojan ya rasu ne a gaban wata mata yayin da suke cikin wata alaƙa ta sirri, da misalin ƙarfe 4:05 na asuba a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Tsohon jami’in DSS ɗin ya ce matar da ƙanwarta, wadda ita ce budurwar Abacha, sun isa Aso Rock, a ranar da lamarin ya faru. A cewar Amachree, budurwar Abacha ta bar ƙanwarta a fadar tare da marigayin janar ɗin.
Yadda Abacha ya bar duniya
Wani bangare na littafin na cewa:
“Da misalin ƙarfe 2:40 na asuba, jim kaɗan bayan Janar Useni ya tafi, budurwar Abacha, wata ƴar kabilar Igbo (ba a bayyana sunanta ba), ta iso Gidan Baƙi na Aso Rock daga Hotel ɗin Nicon Nogs Hilton,”

Kara karanta wannan
Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2
“Tare da ita akwai ƙanwarta, wata ma’aikaciyar lafiya wadda ta zo Abuja domin halartar wani taro. Shugaban mulkin ƙasar ya sayawa budurwar tasa sabuwar motar SUV, don haka suka yanke shawarar zuwa su gaishe da ‘Oga’.
“Abacha ya nuna sha’awa ga ƙanwarta, kuma bayan ɗan lokaci, budurwar ta koma otel, ta bar ma’aikaciyar lafiyar ita kaɗai tare da shugaban ƙasar."
“Da misalin ƙarfe 4:05 na asuba, yayin da suke cikin kusanci, ma’aikaciyar lafiyar ta lura cewa Abacha ya daina motsi. Ta kira shi, amma bai amsa ba kuma jikinsa ya yi tauri. Ta duba bugun zuciyarsa, amma ba ta ji komai ba."
“Cikin firgici, ta yi sauri ta saka tufafinta sannan ta bar gidan baƙin, ta gaya wa sojan da ke gadin wurin cewa ‘Oga’ ya nemi a samo mata mota domin ta koma otel ɗinta."
“Sojan, wanda bai san girman lamarin ba, ya shirya mata abin tafiya cikin gaggawa. Ta koma Hilton, kuma bayan ta gaya wa yayarta abin da ya faru, aka kai ta filin jirgin sama na Abuja cikin sauri domin ta kama jirgin Okada Airline na ƙarfe 7:00 na safe zuwa Legas."
“Wannan shi ne damar da Manjo Al-Mustapha ya rasa. Lokacin da aka sanar da shi cewa Abacha na cikin wani hali da misalin ƙarfe 5:00 na asuba, ya tambayi wanda yake tare da janar ɗin. Aka gaya masa game da ƙanwar budurwar, wadda aka sauke a Hilton."
“Nan take aka sanar da Hukumar Tsaro ta Ƙasa (SSS), kuma jami’anta suka je Hilton domin kama budurwar, amma ma’aikaciyar lafiyar da suke matuƙar buƙata ta riga ta kama hanya zuwa Legas.”
An yi mata tambayoyi
Amachree ya ce ya yi wa matar tambayoyi a Ogudu, Legas, bayan daraktan ayyuka na hedikwatar DSS ta ƙasa ya kira shi, jaridar TheCable ta kawo labarin.
A yayin tambayoyin, tsohon mataimakin daraktan DSS ɗin ya ce kalmomin farko da ma’aikaciyar lafiyar ta faɗa su ne: “Ba ni na kashe shi ba, ya mutu a kaina.”
Ya ƙara da cewa bayanin matar ya saɓa wa “ra’ayoyin makirci da karairayi” da suka dabaibaye mutuwar Abacha, ciki har da labaran “yan matan Indiya da aka shigo da su” da kuma “tuffa mai guba”.

Source: Getty Images
Littafin ya ci gaba da cewa:
“Tawagata ta gano ta kuma kawo ta ofishina. Ni da kaina na yi mata tambayoyi,”
“Abu na farko da ta ce min shi ne: ‘Ba ni na kashe shi ba, ya mutu a kaina.’ Bayan ta ba da cikakken bayani, na kira daraktan da ke Abuja, kuma nan take aka mayar da ita ta kan jirgin sama."
“Bayanin ma’aikaciyar lafiyar, wadda a fili yake Abacha ya gamu da bugun zuciya sakamakon kusancin da suka yi, shi ne ainihin abin da ya faru, kuma ya kawo ƙarshen ra’ayoyin makirci da rabin-gaskiyar da suka bazu.”
Dan Abacha ya kare mahaifinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sadiq Sani Abacha, ya fito fili ya kare mahaifinsa dangane da yadda wasu ke siffanta shi a tarihin siyasar Najeriya.
Sadiq S. Abacha ya bayyana cewa duk da sukar da ake yi wa mahaifinsa, tarihi zai tabbatar da cewa ya kasance shugaba nagari.
Asali: Legit.ng


