Abin Boye Ya Fito: Yadda Aka Cusa N1.3bn na Ma'aikatar Bogi a Kasafin 2026
- Adeyemi Matthew Adeniyi ya yi magana kan yadda hukumar bogi ta PFIPC ta shiga cikin kasafin kudin shekarar 2026
- Ya musanta cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila na da hannu kai tsaye wajen ware Naira biliyan 1.3 ga hukumar
- Adeniyi ya ce bai ba jami’an Ofishin Kasafin Kudi cin hanci ba, sai dai ya yi alkawarin samar musu da guraben aiki idan hukumar ta fara aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Adeyemi Matthew Adeniyi, wanda ya kira kansa shugaban hukumar da ake zargin Shugaban Ƙasa ya kafa mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), ya yi magana kan shigarta cikin kasafin kudi.
Adeniyi ya ce jami’an Ofishin Kasafin Kudi ne suka taimaka wajen shigar da hukumar cikin kasafin kudin gwamnatin tarayya bayan an kama shi.

Kara karanta wannan
PFIPC: Kamfanin Amurka ya kawo ɗauki ga shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a Najeriya

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta ce Adeniyi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, a wani bidiyo da aka fitar bayan kama shi.
Ya kuma musanta cewa Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, na da hannu kai tsaye wajen ware Naira biliyan 1.3 da aka ruwaito an tanadar wa hukumar, yana mai cewa shi da kansa ya bi ta hannun jami’an Ofishin Kasafin Kudi wajen kokarin shigar da hukumar cikin kasafin kudin.
Yadda aka shigar da hukumar cikin kasafi
A cewar Adeniyi, ya fara zuwa Ofishin Kasafin Kudi a watan Disamba na 2024 domin neman a shigar da hukumar cikin Kudirin Kasafin Kudi na 2025. Sai dai ya ce an sanar da shi cewa an riga an kammala shirya kasafin kudin.
“Na je Ofishin Kasafin Kudi domin kasafin kudin 2025. Na mika wasika ta da dukkan takardun da ake bukata, amma aka gaya min cewa lokaci ya kure,” in ji shi.
Ya kara da cewa daga bisani jami’an ofishin sun shawarce shi da ya nemi a yi la’akari da hukumar a cikin kasafin kudin 2026, rahoton Vanguard ya nuna hakan.
“Lokacin da kasafin kudin 2025 ya fito ban ga hukumar a ciki ba, sai suka gaya mini cewa yanzu za a mayar da batun zuwa kasafin kudin 2026. Mun ci gaba da tuntubar juna saboda sun ce za a yi la’akari da batun daga baya,” in ji shi.
Adeniyi ya yi zargin cewa wata jami’a ce ta taimaka wajen shirya ganawarsa da Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kudi, wanda daga bisani ya tura shi wajen wani darakta.
A cewarsa, daraktan ya sanar da shi cewa ba za a iya shigar da wannan shawara cikin kasafin kudin 2025 ba, amma ya tabbatar masa cewa za a ci gaba da kokarin shigar da ita cikin kasafin kudin 2026.
Shin Adeniyi ya bayar da cin hanci?
Da aka tambaye shi ko ya ba wani jami’in Ofishin Kasafin Kudi na goro domin saukaka masa wannan aiki, Adeniyi ya musanta hakan, yana mai cewa kawai ya yi alkawarin samar da guraben aiki ne idan hukumar ta fara aiki.

Kara karanta wannan
PFIPC: Yadda 'yan sanda suka bankado ma'aikatar bogi a karkashin gwamnatin Tinubu
“Gaskiya ban ba kowa kudi ba. Abin da na yi alkawari shi ne idan na fara daukar ma’aikata, zan iya taimaka musu wajen samun guraben aiki,” in ji shi.
Ya ce duk wani kokari na shigar da hukumar cikin kasafin kudin ya tsaya ne bayan an kama shi.

Source: Facebook
Adeniyi ya aika sako ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu.
A cikin sakon nasa, Adeniyi Adeyemi ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken rikicin da ya dabaibaye hukumar.
Asali: Legit.ng
