Tinubu Ya Amince a Dauki Sababbin Ma'aikata 3,252, Minista Ya Yi Karin Bayani
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da fara ɗaukar malamai 3,252 na ƙungiyoyin iyaye da malamai (PTA) aiki a gwamnatin tarayya bayan tantance su
- Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce matakin zai rage ƙarancin malamai a Kwalejojin Haɗin Kai da na Fasaha tare da inganta ilimi
- Gwamnati ta ce malamai da suka kwashe kusan shekaru 25 suna koyarwa a makarantu za su samu damar shiga aikin gwamnati bisa ƙa'ida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara aikin ɗaukar malamai 3,252 na ƙungiyoyin iyaye da malamai (PTA) aiki a gwamnatin tarayya.
A cewar fadar shugaban kasa, wannan zai magance matsalar ƙarancin malamai a Kwalejojin Haɗin Kai da Kwalejojin Fasaha na gwamnatin tarayya.

Source: Twitter
Za a dauki malamai aikin gwamnati
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Ikharo Attah, ya fitar a ranar Alhamis, in ji rahoton Punch.
A cewar ministan, za a ba da fifiko ga malaman PTA da aka tantance, musamman waɗanda suka shafe shekaru da dama suna koyarwa a Kwalejojin Haɗin Kai da Kwalejojin Fasaha ba tare da kasancewa cikakkun ma'aikatan gwamnati ba.
Tunji Alausa ya bayyana cewa amincewar da shugaban ƙasa ya bayar wata babbar nasara ce ga ɓangaren ilimi, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa adadin malamai tare da nuna godiya ga waɗanda suka sadaukar da kansu wajen koyar da ɗalibai tsawon shekaru.
Ya ce:
"Wannan shugaban ƙasa ne da yake kula da makomar Najeriya da kuma ilimin 'ya'yan ƙasa. Ya amince da ɗaukar malamai aiki, inda za a ba da fifiko ga malaman PTA da aka tantance."
Ministan ya ƙara da cewa da dama daga cikin malaman sun yi kusan shekara 25 suna aiki a makarantu, kuma yanzu za su samu damar shiga aikin gwamnati bisa ƙa'ida.
Yadda aka tantance malaman
Alausa ya bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan wani cikakken aikin tantancewa da kwamitin haɗin gwiwar ma'aikatun gwamnati ya gudanar a Kwalejojin Haɗin Kai na tarayya.
Ya ce an tantance malamai 3,252 da suka haɗa da jami'an ilimi, mataimakan jami'an ilimi da masu koyar da darussan fasaha, domin a shirya su zuwa aikin gwamnati bayan sun cika sauran sharuddan doka.
Vanguard ta rahoto ministan ya ce wannan mataki zai taimaka wajen inganta rabon malamai da ɗalibai tare da ba da lada ga malaman da suka ci gaba da aiki duk da ƙalubalen da suka fuskanta tsawon shekaru.

Source: Twitter
Gwamnati ta yi ƙarin haske
A cewar Alausa, haɗa ƙwararrun malaman PTA cikin tsarin aikin gwamnati zai taimaka wajen adana ƙwarewar da suka samu, ƙarfafa koyarwa a azuzuwa da kuma inganta sakamakon karatun ɗalibai a Kwalejojin Haɗin Kai.
Ya bayyana cewa shirin na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na inganta ingancin malamai da mayar da makarantun gwamnatin tarayya cibiyoyin nagartar ilimi.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa ma'aikatar ilimi za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin gwamnati domin kammala duk sauran matakan doka kafin a bayar da takardun ɗaukar aikin na ƙarshe.
WAEC ta saki sakamakon jarabawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta 2026, inda sama da ɗalibai miliyan 1.2 suka samu aƙalla darussa biyar.
Ɗalibai za su fara samar da PIN da Serial Number a shafin WAEC kafin su shiga shafin duba sakamako domin ganin sakamakonsu cikin sauƙi.
Jarabawar ta gudana tsakanin Afrilu da Yuni 2026, yayin da makarantu da dama suka yi amfani da tsarin jarabawar kwamfuta tare da tsarin rubutu.
Asali: Legit.ng


