ICPC Ta Cafke Gbajabiamila kan Badakalar PFIPC? Hukumar Ta Yi Bayani

ICPC Ta Cafke Gbajabiamila kan Badakalar PFIPC? Hukumar Ta Yi Bayani

  • Hukumar ICPC ta ce Femi Gbajabiamila ya je gabanta ne bisa gayyatar masu bincike, ba wai an kama shi ba
  • Hukumar ta ce shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya ba da bayaninsa kan binciken hukumar PFIPC da ake zargin ta ƙarya ce
  • Binciken ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu, yayin da Majalisar Wakilai da ita ma ke gudanar da nata bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Sauran Laifukan da Suka Shafi Hakan (ICPC) ta yi magana kan batun ta cafke Femi Gbajabiamila.

ICPC ta karyata rahotannin da ke cewa an kama, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, kan badakalar hukumar PFIPC.

ICPC ba ta cafke Gbajabiamila ba
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

ICPC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, 21 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Badakalar biza: EFCC ta dauko batun bincikar shugabar hukumar NIS

ICPC ba ta cafke Femi Gbajabiamila ba

Hukumar ta ce Gbajabiamila ya je hedikwatarta da ke Abuja ne domin amsa gayyatar masu bincike, ba wai an kama shi ba.

Sanarwar na zuwa ne bayan rahotannin cewa Gbajabiamila ya je hedikwatar hukumar ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 dangane da binciken da ake gudanarwa kan PFIPC.

A cikin sanarwar, hukumar ta ce shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya je ne da kansa domin amsa tambayoyin masu bincike.

“Hukumar ta tabbatar da cewa ziyarar shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ta kasance ne bisa gayyatar masu bincikenta kuma hakan ya yi daidai da ƙoƙarinta na ci gaba da tattara dukkan bayanan da suka dace kan lamarin."
“Ba a kama shi ba; kawai ya amsa gayyata ne da kansa,” in ji sanarwar.

Binciken ICPC kan hukumar PFIPC

Hukumar ta ce Shugaba Bola Tinubu ya umarce ta da ta binciki yadda ake zargin PFIPC ta yi aiki daga Sakatariyar Tarayya da ke Abuja na tsawon kusan shekaru biyu ƙarƙashin Adeniyi Adeyemi.

Kara karanta wannan

An zo wajen: ICPC ta titsiye Gbajabiamila kan badakalar hukumar PFIPC

A cewar ICPC, Gbajabiamila ya isa hedikwatar hukumar da yammacin Litinin, ya amsa tambayoyin masu bincike sannan ya tafi bayan ya ba da bayaninsa.

"ICPC ta tabbatar da cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya kasance a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Litinin, 20 ga Yuli, 2026, domin ba da bayani dangane da binciken da ake ci gaba da gudanarwa kan hukumar PFIPC." in ji sanarwar.

Hukumar ta ƙara da cewa binciken da ake gudanarwa kan hukumar da ake zargin ta ƙarya ce yana ci gaba da gudana, kuma za ta fitar da ƙarin bayani.

ICPC ba ta cafke Gbajabiamila ba
Shugaban hukumar ICPC, Dr. Musa Aliyu Hoto: ICPC Nigeria
Source: Facebook

Yadda PFIPC ta shiga kasafin kudi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu bayanai kan yadda aka sanya hukumar bogi ta PFIPC a kasafin kudin shekarar 2026.

Adeniyi Adeyemi mai ikirarin shugabantar hukumar, ya ce jami’an Ofishin Kasafin Kudi ne suka taimaka wajen shigar da hukumar cikin kasafin kudin gwamnatin tarayya bayan an kama shi.

A cewar Adeniyi, ya fara zuwa Ofishin Kasafin Kudi a watan Disamba na 2024 domin neman a shigar da hukumar cikin Kudirin Kasafin Kudi na 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng