Ministan Tsaro Christopher Musa Ya Yi Murabus? Gwamnati Ta Yi Bayani

Ministan Tsaro Christopher Musa Ya Yi Murabus? Gwamnati Ta Yi Bayani

  • Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan rahotannin cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), zai yi murabus daga mukaminsa
  • Ofishin ministan tsaron ya fito ya yi bayani filla-filla kan jita-jitar wadda aka rika yadawa a wasu kafafen sadarwa
  • Gwamnatin Tarayya ta bukaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su rika tabbatar da bayanai daga hukumomin da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), yana shirin yin murabus daga mukaminsa.

A cikin wata sanarwa da Ofishin Ministan ya fitar ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026,ya bayyana rahotannin a matsayin "kirkirarren labari” tare da kira ga jama’a da su yi watsi da su.

Christopher Musa bai yi murabus ba
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa mataimakiyar Ministan kan harkokin yaɗa labarai, Leah Katung-Babatunde, ce ta sanya wa sanarwar hannu mai taken “Jita-jitar Karya Kan Mai Girma Ministan Tsaro”.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2026: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da boye Naira tiriliyan 12.8

Gwamnati ta karyata jita-jita kan Christopher

Sanarwar ta ce ofishin Ministan ya samu labarin wasu rahotanni da ke yawo a intanet, wadanda ke ikirarin cewa Janar Musa ya bayyana aniyarsa ta sauka daga mukaminsa.

“Muna bayyanawa ba tare da wata tantama ba, cewa wadannan jita-jita karya ce tsantsa da aka kirkira saboda mugunta,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), OFR, na ci gaba da mai da hankali sosai kan nauyin da ke kansa, tare da jajircewa wajen aiwatar da ajandar Gwamnatin Tarayya kan tsaron kasa da harkokin tsaro.

Sanarwar ta ce Ministan ya ci gaba da sadaukar da kansa wajen kula da dabarun tsaron kasa da kuma sauke nauyin da aka dora masa, rahoton jaridar Blueprint ya tabbatar da hakan.

An yi kira ga jama’a

Gwamnati ta kuma bukaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su tabbatar da sahihancin bayanai ta hanyoyin hukuma kafin su wallafa ko yada su.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Yadda aka cusa N1.3bn na ma'aikatar bogi a kasafin 2026

“An bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labarin karya. Muna gargadin kafafen yaɗa labarai da masu amfani da intanet da su daina yada bayanan da ba a tabbatar da su ba, tare da neman karin bayani daga ofishin Ministan kan duk wani batu da ya shafe shi,” in ji sanarwar.

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada cewa Ministan Tsaro na nan kan mukaminsa kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa.

Gwamnati ta musanta murabus din Christopher Musa
Ministan tsaro na Najeriya, Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Christopher Musa ya yi fallasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan tsaro , Christopher Musa, ya bayyana rukunin mutane biyu da ke kara rura wutar matsalar tsaro kasar nan.

Christopher Musa ya ce masu bada bayanai da ake kira infoma da masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya ne suka sa matsalar tsaro ta ci gaba da ƙamari a ƙasar.

Ya ce ba zai yiwu a kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba idan har jama’a ba su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng