Manyan Labarai A Yau
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah-wadai da kisan mai magana kan siyasa Ibrahim Khalil Dan Shagamu a Kano, inda ya buƙaci gwamnatin jihar ta gudanar da bincike.
Akalla mutane 24 sun mutu a wasu garuruwa biyu a jihar Ondo bayan sun sha wani ruwan ganye, yayin da hukumomi ke gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar.
An kashe fitaccen mai sharhin siyasa da ke Kano, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a gidansa da ke jihar Kano, lamarin da ya jefa mabiyansa da al'ummar jihar cikin jimami.
Ƙungiyar Houthi ta kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan biranen Khamis Mushait, Abha da Jizan a kudu maso yammacin Saudiyya.
Ƙungiyar goyon bayan Bola Tinubu ta nuna fargabar yiwuwar tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ya aikata abin da zai saba wa jam’iyyar APC a 2027.
Yan takarar ADC na gwamna a jihohin Arewa maso Yamma bakwai sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta tsaro, tattalin arziki da jin daɗin al’umma.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya musanta cewa ya ce za a azabtar da ’yan Arewa daga Janairu zuwa Mayu idan Tinubu ya sha kaye a zaɓen 2027.
Rahotanni daga majiyoyi msu alaka da kungiyar Houthi ya ruwaito cewa jiragen yakin Saudiya na kai hare-haren sama a wasu larduna daban-daban na kasar Yemen.
Mutane biyar sun mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu ya faɗi a wani filin jirgi mai nisa a jihar Sarawak da ke Malaysia. Hukumomi za su yi bincike.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari