Kaduna da Jihohin Najeriya 16 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa a cikin Kwanaki 7

Kaduna da Jihohin Najeriya 16 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa a cikin Kwanaki 7

  • Hukumar NIHSA ta gargadi jihohi 17 da su shirya saboda yiwuwar ambaliya daga ranar 21 zuwa 27 ga Yulin 2026
  • Bauchi, Edo, Imo, Kaduna, Plateau da Benue na cikin jihohin da aka ce za su fuskanci matsakaicin hadarin ambaliya a mako guda
  • NIHSA ta bukaci jama'a su kaurace wa yankunan da ke kusa da koguna tare da guje wa ketare hanyoyin da ruwa ya mamaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja - Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Kasa (NIHSA) ta gargadi cewa jihohi 17 za su fuskanci yiwuwar ambaliya tsakanin ranar 21 zuwa 27 ga watan Yulin 2026.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin sabon rahoton ta na ambaliyar ruwa (Alert No.: NFA-2026-200), inda ta ce akwai matsakaicin hadarin ambaliya a wasu sassan kasar.

An lissafa jihohin Najeriya 17 da za su gamu da ambaliya daga 21 zuwa 27 ga Yulin 2027
Ambaliyar ruwa ta shanye wani gari da ke a Maiduguri, jihar Borno a 2024. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Jihohin da ke cikin hadarin ambaliya

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Darakta Janar kuma Babban Jami'in Hukumar NIHSA, Arc Umar Mohammed, ya ce jihohin da ke cikin hadarin sun hada da Bauchi, Edo, Imo, Kaduna, Plateau da Benue, tare da karin jihohi 11, in ji rahoton Vanguard.

Ya ce rahoton ya nuna yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu manyan koguna da filayen da ke kusa da su, lamarin da ke bukatar daukar matakan kariya cikin gaggawa.

Mohammed ya bayyana cewa cibiyoyin lura da matakan ruwa sun gano cewa ruwa ya haura matakin gargadi a wasu wurare.

Ya ce hakan ya shafi tashoshin lura da ruwa da ke Saminara a Kogin Karam, Waya Dam Site a Kogin Waya da Amber a Kogin Amber.

A cewarsa, tashoshin lura da ruwa guda 16 sun nuna karuwar matakin ruwa, abin da ke nuni da yiwuwar ambaliya a yankunan da ke kusa da koguna.

Garuruwa, kadarori na cikin hadari

Rahoton ya nuna cewa:

  • A jihar Bauchi, al'ummomi 1,841, makarantu 145, cibiyoyin lafiya 101 da kasuwanni takwas na cikin hadari.
  • A Edo, al'ummomi 148, makarantu 131 da cibiyoyin lafiya 123 na iya fuskantar ambaliya.
  • A Imo, al'ummomi 415, makarantu 423, cibiyoyin lafiya 198 da gonaki sama da hekta 75 na cikin yankunan da ke cikin hadari.
  • A Plateau, al'ummomi 205, makarantu 137 da gonaki masu fadin hekta 64 na iya shafa.
  • A Kaduna da Benue ma akwai yankunan da rahoton ya nuna suna cikin hadari.

Kara karanta wannan

ADC ta nemi gwamnati ta fito da bayanai kan yadda aka kashe N17.5tr a NNPCL

Shawarwarin hukumar NIHSA

Hukumar ta bukaci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), hukumomin SEMA, shugabannin kananan hukumomi da na al'ummomi su dauki matakan kariya cikin gaggawa.

Ta bukaci a kwashe jama'a, dabbobi da kayayyaki daga yankunan da ke kusa da koguna zuwa wuraren da suka fi aminci, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Haka kuma, ta ce ya kamata a tanadi kayan agajin gaggawa, magunguna, ruwan sha da kayan abinci domin taimakawa wadanda ambaliyar za ta iya shafa.

NIHSA ta gargadi jama'a da kada su yi yunkurin ketare hanyoyi, gadoji ko wuraren da ruwa ya mamaye, tare da bukatar a rika tsaftace magudanan ruwa domin saukaka gudun ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com