"Zan Sanya": Alkawarin da Remi Tinubu Ta Dauka kan Tazarcen Mijinta a 2027

"Zan Sanya": Alkawarin da Remi Tinubu Ta Dauka kan Tazarcen Mijinta a 2027

  • Oluremi Tinubu ta ce za ta sanya zannuwan Akwete idan mijinta, Shugaba Bola Tinubu, ya samu wa’adi na biyu
  • Uwargidan Shugaban Ƙasa ta sanar da bayar da gudunmawar Naira biliyan biyu domin farfaɗo da masana’antar saka atamfar Akwete
  • Ta bukaci ’yan Najeriya su rungumi kayan gargajiya da aka kera a gida domin tallafa wa masu sana’ar saka zane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta yi alkawari kan tazarcen mijinta, mai girma Shugaba Bola Tinubu.

Remi Tinubu ta ce za ta sanya zannuwan Akwete idan mijinta, Shugaba Bola Tinubu, ya samu wa’adi na biyu a matsayin shugaban Najeriya.

Remi Tinubu za ta sanya zannuwan Akwete
Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu na jawabi Hoto: Umar Namadi
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa ta bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yulin 2021 yayin ziyararta ta farko zuwa wurin masu sana’ar saka atamfar Akwete da ke jihar Abia.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Wane alkawari Remi Tinubu ta dauka?

Remi Tinubu ta kuma sanar da bayar da gudunmawar Naira biliyan biyu domin farfaɗo da masana’antar saka atamfar Akwete.

“Idan Allah ya sake ba mijina damar komawa karo na biyu, zan sanya riga da zani da aka yi da Akwete. Zan sanya su ne saboda audugar tana da laushi kuma tana barin iska ta ratsa."
“Na ga matasa a cikin iyalansu suna yin wannan sana’ar. Don haka sana’a ce da ake gadar da ita daga kaka kakanni." in ji ta.

Oluremi ta yabawa masu sana’ar Akwete

Tinubu ta yaba wa matan ƙungiyar haɗin gwiwar saboda jajircewarsu da juriyarsu wajen kare wannan sana’a da kuma gadar da ita ga na bayansu.

Ta kuma bukaci ’yan Najeriya su rungumi kayan gargajiya na Igbo da aka kera da wannan zane domin tallafa wa masu sana’ar saka zane na cikin gida.

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce ta gudanar da ziyarar ne ba tare da wani tsari na musamman ba, inda ta fi son samun lokaci tare da matan maimakon bin wani shirin da aka tsara tun farko.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Ta ce ba ta zo da jawabin da ta shirya ba saboda manufar ziyarar ita ce yin hulɗa ta musamman da matan, ba wani taron hukuma ba.

Ta yabawa Gwamna Alex Otti

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma gode wa Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, inda ta bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

Ta tuna cewa a baya ta taɓa tuntuɓar matar gwamnan domin tambaya game da al’adar saka atamfar Akwete. Ta ce tana godiya ga Allah da a ƙarshe ziyarar ta samu damar tabbata duk da jinkirin da aka samu.

“Abin da kawai nake so shi ne na haɗu da waɗannan matan, kuma zan ba da labarin hakan. Amma muka ci gaba da tafiya, sai mijina ya faɗi wani abu. Ya ce na fara takaici. Na ce, Otti mutumin kirki ne."
“Mutumin kirki ne ƙwarai. Ina ganin hakan, kuma ina son na gode maka. Kuma na tuna lokacin da nake kiranka ina neman matarka saboda batun Akwete. Amma ina godiya ga Allah da muka kasance a nan. Duk wannan tarihin, yanzu muna nan,” in ji ta.
Remi Tinubu ta je jihar Abia
Remi Tinubu yayin ziyararta zuwa jihar Abia Hoto: @alexottiofr
Source: Twitter

Ta ƙara kira ga ’yan Najeriya da su riƙa sayen kayan da aka kera a cikin gida domin kare sana’o’in gargajiya da kuma inganta rayuwar masu saka zane da ke zaune a ƙauyuka.

Kara karanta wannan

An fitar mukamai 26 da Tinubu ya ba mutane daban daban a Najeriya

Rokon Remi Tinubu ga manyan mawaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga fitattun mawakan Afrobeats, Burna Boy, Davido da Asake, da su kafa gidauniyoyi domin taimaka wa marasa galihu a Najeriya.

Uwargidan shugaban kasar ta ce Najeriya na da attajirai masu yawa, amma akwai buƙatar su ƙara tallafa wa mabukata saboda nauyin da ke kan gwamnati yana da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng