Trump Ya Aiko da Rubutacciyar Wasika ga Shugaba Tinubu

Trump Ya Aiko da Rubutacciyar Wasika ga Shugaba Tinubu

  • Donald Trump na Amurka ya yaba wa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa wajen yaki da ’yan ta’adda
  • Shugaban na Amurka ya ce dangantakar Amurka da Najeriya na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci
  • Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Najeriya kan hadin gwiwar tsaro domin dakile ayyukan 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan tsayayyen matsayinsa “a madadin al’ummar Najeriya”.

A cikin wata wasika da ya aikawa Shugaba Tinubu, Trump ya yaba da kudurin shugaban na “magance matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman tashin hankalin da ke shafar al’ummomin Kirista”.

Trump ya rubuto wasika ga Tinubu
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Hadimin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

"Ya fi su": Gwamna Sule ya fadi fannin da Tinubu ya yi wa Atiku, Obi fintinkau

Dangantakar Amurka da Najeriya

Dangantakar Amurka da Najeriya ta kara bunkasa a baya-bayan nan, inda kasashen biyu ke aiki kafada da kafada a muhimman fannoni, musamman wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan Najeriya.

A watan Nuwamban bara, Shugaba Trump da Shugaba Tinubu sun amince da kafa wata kungiyar aiki ta hadin gwiwa wadda masu ba shugabannin kasashen biyu shawara kan harkokin tsaro za su jagoranta.

Ta hanyar aikin kungiyar, kasashen biyu sun amince da wasu matakai da suka hada da horaswa, musayar bayanan sirri da gudanar da ayyukan hadin gwiwa domin dakile ayyukan ’yan ta’adda.

Wani babban abin da ya samu daga wannan hadin gwiwa shi ne harin hadin gwiwa da aka kai ranar 16 ga Mayu kan maboyar kungiyar ISIS a yankin Tafkin Chadi, wanda ya yi sanadiyyar kashe babban jagoran kungiyar, Abubakar Al-Minoki, da wasu da dama daga cikin kwamandojinsa.

A makon da ya gabata, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka, Frank Garcia, ya ziyarci Abuja, inda ya gana da manyan jami’an gwamnati tare da yin alkawarin karfafa hadin gwiwa tsakanin Abuja da Washington DC a fannin tsaro da sauran bangarorin hadin gwiwa.

Kara karanta wannan

"Zan sanya": Alkawarin da Remi Tinubu ta dauka kan tazarcen mijinta a 2027

Cikakkiyar wasikar Trump ga Tinubu

Ga cikakkiyar wasikar da aka rubuta ranar 6 ga Yuli, 2026:

“Na gode da wasikarka mai cike da tunani. Kalaman alherinka na da matukar muhimmanci a gare ni, kuma ina yabawa da tsayayyen jagorancinka a madadin al’ummar Najeriya."
"Ina yabawa da kudurinka na magance matsalolin da ke addabar kasarka, musamman tashin hankalin da ke shafar al’ummomin Kirista, kuma babban abin alfahari ne a gare ni na tsaya tare da kai wajen yaki da ’yan ta’adda da kuma tabbatar da Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta kara karfi da wadata."
“Dangantakar Amurka da Najeriya na da matukar muhimmanci a daidai lokacin da rikici ya bazu a Yammacin Afirka da sauran sassan duniya. Dukkanmu muna da manufa guda ta tunkarar ta’addanci ta kowace siga, kuma taswirar hadin gwiwar tsaro ta tarihi tsakanin Amurka da Najeriya ta shekarar 2026 ta samar da ingantaccen tsari da za mu cimma wannan buri.
“Ina alfahari da tura rundunar sojojin musamman ta Amurka, wadanda ke cikin fitattun rundunonin soji a duniya, domin ba jarumai maza da mata na rundunar sojin Najeriya kwarewa, kayan aiki da bayanan sirrin da suke bukata wajen kare kasarku da tabbatar da tsaron ’yan kasa, musamman masu bin addini wadanda ake kai wa hare-hare. Ina fatan za mu ci gaba da tattaunawa a tsawon lokacin shugabancina.”

Kara karanta wannan

Kamfanin da Atiku ya dauko haya sun fara kai bayanan Tinubu wajen Trump a Amurka

- Donald Trump

Trump ya rubuto wasika ga Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Trump ya yi barazana ga kasar Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya aika da sakon gargadi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaba Trump ya yi barazanar kai hari kan gadoji da tashoshin samar da lantarki na Iran idan har ta farmaki jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng