Auren Gata: Hisbah Ta Gano Makircin da Ake Shiryawa, Ta Aika Sakon Gargadi

Auren Gata: Hisbah Ta Gano Makircin da Ake Shiryawa, Ta Aika Sakon Gargadi

  • Hukumar Hisbah ta Kano ta gargadi jama’a kada su biya kudi domin shiga shirin auren gata da za a gudanar a jihar
  • Hisbah ta ce babu wani jami’inta ko wakilin gwamnati da aka ba izinin karbar kudi daga masu son shiga shirin na auren gata
  • Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 1.5 domin tallafa wa ma’aurata 1,500 a shirin da take yi na gudanar da auren gata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi gargadi ga jama’a kan shirin auren gata da ake shirye-shiryen gudanarwa.

Hisbah ta gargadi jama'a da kada su biya kudi ga duk wani mutum da ya nemi karbar kudi domin saka sunayensu cikin shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shirin gudanarwa.

Hisbah ta yi gargadi kan auren gata a Kano
Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Dr. Aminu Ibrahim Muhammad Daurawa
Source: Facebook

Mataimakin shugaban hukumar, Dr Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayar da wannan gargadin ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026 a Kano, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Wani uba da ƴarsa sun rasu bayan sun fada rijiya a Kano

Ya yi gargadin ne bayan samun rahotannin cewa wasu mutane na neman kudi daga masu neman cin gajiyar shirin da sunan taimaka musu wajen yin rajista.

Gwamnati ta dauki nauyin shirin

Aminuddeen ya ce gwamnatin jihar ce ta dauki nauyin shirin gaba daya, inda Gwamna Abba Yusuf ya amince da samar da kayan aure, kayan daki, kudin jigilar kayan dakin da kuma jarin fara sana’a ga wadanda za su amfana.

Ya ce babu wani jami’in hukumar Hisbah ko wakilin gwamnati da aka ba izinin karbar kudi daga duk wanda ke neman shiga shirin.

Ya bukaci duk wanda wani ya tuntuba yana neman kudi domin shiga shirin da ya kai rahoton lamarin nan take ga hukumar Hisbah ko hukumomin tsaro da abin ya shafa domin gudanar da bincike da daukar matakin da ya dace.

“Gwamna ya biya komai. Kada kowa ya biya komai domin shirin gaba daya kyauta ne,” in ji shi.

Ma’aurata 1,500 za su amfana

Shirin auren gata na jihar Kano na daga cikin shirye-shiryen tallafin jama’a na gwamnatin Abba Kabir Yusuf da aka tsara domin tallafa wa ma’auratan da ba su da karfin hali da kuma rage musu nauyin kudin aure.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

Daily Trust ta ruwaito cewa shirin auren gata mai zuwa a Kano zai hada ma’aurata 1,500, yayin da gwamnati ta amince da ware Naira biliyan 1.5 domin gudanar da shirin.

Shirye-shiryen gudanar da bikin sun kankama, ciki har da gudanar da gwaje-gwajen lafiya na tilas da shirye-shiryen kayan aiki, yayin da ake jiran Gwamna Yusuf ya sanar da ranar bikin a hukumance.

Hisbah ta yj gargadi kan auren gata
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hisbah ta kafa sabuwar doka a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta Kano ta sanar da haramta sana'ar sauke da rarraba fina-finai ta amfani da wayoyin salula a fadin jihar.

Hukumar ta bayyana cewa matakin wani bangare ne na kokarinta na kare tarbiyyar al'umma da kuma inganta koyarwar addinin Musulunci a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng