An Zo Wajen: Israila Ta Yi Maganar Shiga Sabon Yakin Amurka da Iran

An Zo Wajen: Israila Ta Yi Maganar Shiga Sabon Yakin Amurka da Iran

  • Bezalel Smotrich ya ce yaƙin Amurka da Iran ya fi amfani ga Isra’ila, kuma kasarsa ba za ta shiga cikinsa ba a yanzu
  • Ministan kuɗin na Isra’ila ya ce yaƙin na yi wa ƙasarsa amfani matuƙa muddin sojojin Isra’ila ba su shiga ba
  • Bezalel Smotrich ya ce burin Isra’ila shi ne raunana gwamnatin Jamhuriyar musulunci ta Iran har ta kai ga kifar da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Israila - Ministan kuɗin Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi, Bezalel Smotrich, ya yi magana kan sabon yakin Iran da Amurka.

Bezalel Smotrich ya bayyana cewa yaƙin da Amurka ta sake far wa Iran shi ne mafi kyawun yanayi ga Isra’ila, muddin Isra’ilawa ba su shiga yaƙin da kansu ba.

Israila ba za ta shiga yakin Amurka da Iran ba
Shugaba Donald Trump da Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Kan News ta sanya hirar da aka yi da Ministan kudin na Israila a ranar Talata, 21 ga watan Yulin 2026 a shafinta na X.

Kara karanta wannan

"Ya mutu yana kaina"; Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar Janar Abacha

Israila ba za ta shiga yakin Amurka-Iran ba

Ya bayyana hakan ne a taron Katif Conference for National Responsibility, wani taro da ake gudanarwa duk shekara domin ingiza komawar matsugunan Isra’ila da aka kafa ba bisa ƙa’ida ba zuwa Gaza.

“Isra’ila ba ta da wata fa’ida wajen shiga wannan yaƙin, halin da ake ciki a yanzu shi ne mafi alheri a gare mu,”

- Bezalel Smotrich

Smotrich ya sha yin kira da a mamaye yankin Gaza, a kafa mulkin soji sannan a sake kafa matsugunan Isra’ila a yankin, yayin da yake kira da a kori Falasɗinawa daga gidajensu.

Yadda yaƙin Iran ya fara

Isra’ila da Amurka sun fara yaƙin ne da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026 bayan Isra’ila ta matsa wa Washington lamba ta shiga rikicin.

Hakan ya sa Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a faɗin yankin.

A farkon wannan watan ne aka sake sabunta yaƙin, bayan Amurka ta kai hare-hare kan wasu wurare a Iran, yayin da Iran ta kai hare-hare kan sansanonin Amurka a sassa daban-daban na yankin. Ya zuwa yanzu, Isra’ila ba ta shiga wannan sabon zagayen yaƙin ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya haramta zabe kwata kwata, zai cigaba da mulki a Nicaragua

Israila na son cimma manufofinta

Sai dai Smotrich ya bayyana cewa Isra’ila na son yaƙin ya cimma manufofinta na dabarun tsaro da siyasa.

“Dole ne mu tuna cewa babban burin Isra’ila, ba lallai ne ya zama na Amurka ba, shi ne raunana da durƙusar da gwamnatin Iran, har ta kai ga kifar da ita,” in ji shi.

Ministan kudin na Israila ya ce lalata tattalin arzikin Iran ita ce hanya mafi inganci wajen cimma wannan buri.

“A halin yanzu, hauhawar farashi a Iran ya kai kashi 85 cikin 100, yayin da hauhawar farashin abinci ya haura kashi 134 cikin 100 cikin jimillar watanni huɗu, sannan ana sayar da rial ɗin Iran kan farashin rial miliyan 1.9 kan dala ɗaya kuma farashin na ci gaba da tashi,” in ji shi.
Smotrich ya ce Israila ba za ta shiga yaki da Iran ba
Ministan kudin Israila, Bezalel Smotrich Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Isra’ila ba za ta shiga yaƙin ba

Daga bisani, Smotrich ya sake jaddada cewa bai kamata Isra’ila ta shiga sabon yaƙin ba, yana mai cewa:

"Halin da ake ciki a yanzu yana da kyau a gare mu, kuma babu wata fa’ida wajen tura kanmu cikin rikicin”.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida; 'Yan sanda sun yi wa shugaban hukumar ICPC kwacen kudi

Trump ya magantu kan cafke Netanyahu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan batun cafke Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu.

Shugaba Donald Trump, ya bayyana cewa ba za a kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ba idan ya kai ziyara ƙasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng