Ministan Tsaro Ya Tona Mutanen da Ke Yada Jita Jitar Cewa Ya Yi Murabus

Ministan Tsaro Ya Tona Mutanen da Ke Yada Jita Jitar Cewa Ya Yi Murabus

  • Christopher Musa ya ce ba ya shirin barin mukaminsa, yana mai cewa bai taba tattauna batun yin murabus ba
  • Ministan ya ce rahotannin jita-jitar murabus dinsa sun ba shi mamaki, yana mai barazanar daukar matakin shari’a kan wadanda suka yada su
  • Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gamsu da yadda sojoji ke gudanar da ayyukansu wajen inganta tsaro a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya sha alwashin daukar matakin shari’a kan wadanda ke yada rahotannin jita-jitar cewa ya yi murabus.

Christopher Musa ya bayyana cewa rahotannin sun ba shi “mamaki” kuma bai san inda suka samo asali ba.

Christopher Musa zai dauki matakin shari'a
Ministan Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Janar Musa ya bayyana hakan ne bayan ya fito daga wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, Abuja, a ranar Talata, 21 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro Christoper Musa ya yi murabus? Gwamnati ta yi bayani

“Ba zan je ko’ina ba. Ban taba tattauna wannan batu ba. Ban ma san wanda ya kawo wannan bayani ba. Amma duk wanda ya kasance, za mu dauki matakin shari’a a kansa,” in ji Janar Musa.

Ministan ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 3:00 na rana, sannan ya fita bayan karfe 4:00 na yamma, a daidai lokacin da jita-jitar makomarsa a mukamin ke kara yaduwa.

Janar Musa ya musanta batun murabus

Bayan ganawar, ministan tsaron ya musanta cewa an taba tattauna batun yin murabus, yana mai cewa mutanen da ba sa farin ciki da yadda tsaro ke inganta a karkashin gwamnatin Tinubu ne ke yada rahotannin.

“Ko ma su waye, za mu dauki matakin shari’a a kansu. Na tabbata za mu same su. Za su zo su bayyana wanda ya ba su wannan bayani,” in ji shi.

Ya bayyana jita-jitar a matsayin wani yunkuri na rage amincewar jama’a da nasarorin da gwamnati ke samu a fannin tsaro.

“Mun yi mamaki. Na yi matukar mamaki lokacin da na ga hakan. Ban san daga ina wannan ya fito ba. Amma a kullum za ka sa ran akwai mutanen da ba za su yi farin ciki ba idan abubuwa suna tafiya daidai. Tsaro yana inganta, abubuwa suna kara kyau, kuma a wurinsu wannan abin bakin ciki ne. A kullum suna son su nuna kamar ba haka abin yake ba,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Janar Christopher Musa ya yi magana kan murabus
Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: Defence News Info
Source: Twitter

Tinubu ya gamsu da ayyukan sojoji

Janar Musa ya ce ganawar sirri da Shugaban kasar ta kasance wani taron yau da kullum na yi wa shugaban bayanin halin da ake ciki a fannin tsaro. Ya ce Tinubu ya nuna gamsuwa da yadda sojoji ke gudanar da ayyukansu.

“Na dawo ne daga yi wa mai girma shugaban kasa bayani kan halin da ake ciki a fannin tsaro, kuma yana matukar farin ciki da mu. Za mu ci gaba da yin abin kirki,” in ji shi.

Christopher ya yi maganar rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a iya shawo kan matsalolin tsaro.

Ministan ya bayyana cewa za a kai ga cimma wannan nasara ne idan al'umma suka haɗa kai tare da mara wa jami'an tsaro baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng