Mutuwar Sojojin Amurka Ta Fusata Trump, Ya Yi Babbar Barazana ga Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba
- Donald Trump ya yi barazanar lalata gada ko tashar samar da wutar lantarki a duk lokacin da Iran ta kai hari kan jirgi a mashigar Hormuz
- Shugaba Trump ya kuma bayyana cewa Amurkawa ba sa adawa da yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba.
Shugaban na Amurka ya kuma kara yin barazanar daukar matakin soja mai tsanani kan kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce Trump ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana kai tsaye da manema labarai yayin da yake tafiya zuwa wani bikin karrama sojojin Amurka da suka mutu a yakin da ake yi da Iran a ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026.
“Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba, ba za su mallaki makamin nukiliya ba."
“Saboda haka za mu karrama su, kuma wannan na daga cikin abubuwan da suka fi wahala a yi. A gare ni, yana daga cikin abubuwan da suka fi wahala a yi a matsayina na shugaban kasa.” In ji Trump
Trump ya yi sabon gargadi
Shugaban na Amurka ya kuma fitar da sabuwar barazana kan Iran a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.
Trump ya rubuta cewa idan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba makami kan wani jirgi a mashigar Hormuz, Amurka za ta kai hari tare da lalata gada guda ko tashar samar da wutar lantarki.
Ya ce hakan zai shafi wuraren da ke kusa da Tehran, babban birnin kasar, ko kuma wadanda ke cikin birnin.
Trump ya ce Amurkawa ba sa adawa da yakin
Trump ya shaida wa manema labarai cewa al’ummar Amurka ba sa adawa da yakin da aka kaddamar kan Iran, yayin da ya gargadi kasar cewa hare-haren za su ci gaba.
“Za su biya babban farashi, ana hallaka su,” in ji shi.
Da aka tambaye shi game da farin jinin yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran, musamman yayin da karin sojojin Amurka ke ci gaba da mutuwa, Trump ya ce:
"To, Amurkawa ba sa adawa da yakin.”

Source: Getty Images
Ra’ayin Amurkawa kan yakin
Sai dai kuri’un jin ra’ayin jama’a sun sha nuna cewa yakin da aka kai wa Jamhuriyar Musulunci a watan Fabrairun 2026 ba tare da an tsokane Amurka ba na kara rasa farin jini a tsakanin Amurkawa.
“Amurkawa ba sa son tsadar man fetur, amma ba sa adawa da yakin. Wannan shi ne abin da wani sabon kuri’ar jin ra’ayi ya fito ya nuna karara,” in ji Trump.
Sai dai ba a bayyana wane kuri’ar jin ra’ayi shugaban na Amurka yake magana a kai ba.
Trump ya kulla yarjejeniya da Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Donald Trump na Amurka, Donald Trump, ya amince da wata muhimmiyar yarjejeniya da Masarautar Saudiyya.
Yarjejeniyar, wadda gwamnatin Shugaba Trump ta amince da ita a hukumance, za ta kasance na tsawon shekaru 30.
Asali: Legit.ng

