An Shiga Tashin Hankali: Wani Uba da Ƴarsa Sun Rasu bayan Sun Fada Rijiya a Kano

An Shiga Tashin Hankali: Wani Uba da Ƴarsa Sun Rasu bayan Sun Fada Rijiya a Kano

  • Wani mutum mai shekara 45 ya rasa ransa tare da diyarsa bayan ya shiga tsohuwar rijiya domin ceto ta a kauyen Yancibi na jihar Kano
  • Hukumar Kashe Gobara ta Kano ta ce an dakatar da aikin ceto saboda duhu kafin daga bisani aka gano gawarwakin mutanen biyu
  • Hukumar ta bukaci jama'a su guji shiga rijiyoyi ba tare da kayan kariya ba, tare da kira ga mutane su rika sanar da hukumomin agaji cikin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Kano - An shiga tashin hankali a jihar Kano bayan wani mutum mai shekara 45, Abubakar Abdullahi, ya rasa ransa yayin da yake kokarin ceto diyarsa mai shekara 15, Fiddausi Abubakar.

An ce Fiddausi Abubakar ta fada cikin wata tsohuwar rijiya da ba a amfani da ita a kauyen Yancibi da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano, kuma mahaifinta ya shiga ya ceto, inda shi ma ya mutu a ciki.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

Wani mutumi ya rasu a garin ceto 'yarsa da ta fada rijiya a Kano
Jami'an kashe gobara na kokarin ceto wanda ya fada rijiya a Kano. Hoto: Saminu Yusif
Source: Facebook

Yadda uba ya mutu wurin ceto 'yarsa a Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar ranar Laraba, in ji rahoton Daily Trust.

Sanarwar ta bayyana cewa reshen hukumar da ke Tsanyawa ya samu kiran neman dauki a yammacin ranar Litinin, 21 ga watan Yuli, cewa wani uba da diyarsa sun fada cikin rijiya.

Nan take jami'an kashe gobarar suka isa wurin domin fara aikin ceto. Sai dai hukumar ta ce an dakatar da aikin a daren saboda duhu da kuma wahalar yanayin rijiyar.

An gano gawarwakin uba da 'ya a rijiya

Da safiyar Talata ne wata tawaga daga hedikwatar Hukumar Kashe Gobara ta jihar ta isa wurin domin taimakawa aikin.

A cewar sanarwar, jami'an sun samu nasarar fitar da mutanen biyu daga rijiyar, amma an same su a sume kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana bayan ganin kumfa a Kaduna

Daga nan aka mika gawarwakinsu ga shugaban kauyen Yancibi, Shamsu Sani, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

Uba da 'yarsa sun mutu a cikin rijiya a Kano
Taswirar jihar Kano, inda wani uba ya mutu a garin ceto 'yarsa da ta fada rijiya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin da bincike ya nuna

Binciken farko ya nuna cewa Fiddausi ta fada cikin rijiyar ne bisa kuskure, yayin da mahaifinta ya shiga domin ceto ta, amma shi ma ya makale a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu.

Hukumar Kashe Gobara ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan tare da gargadin jama'a su guji shiga rijiyoyi ko wasu wuraren da ke da hadari ba tare da kayan kariya da suka dace ba.

Haka kuma ta bukaci mutane su rika tuntubar hukumomin agaji cikin gaggawa idan irin wannan hadari ya faru domin kauce wa karin asarar rayuka.

Magidanci ya fada rijiya ya mutu

A wani labari, mun ruwaito cewa, dan shekaru 45, mai suna Yusuf Usman, ya rasu bayan ya fada wata tsohuwar rijiya a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, kuma hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da aukuwar sa a cikin wata sanarwa da ta ya fitar.

A cewar sanarwar, hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:13 na safe daga ɗaya daga cikin ma’aikatanta mai suna Kabiru Tata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com