Matakai Masu Sauki da Za Ku Bi don Bude Layin MTN da Aka Rufe saboda Matsalar NIN

Matakai Masu Sauki da Za Ku Bi don Bude Layin MTN da Aka Rufe saboda Matsalar NIN

Abuja - Samun sakon cewa an toke layin wayar ka na MTN ba karamin tashin hankali ba ne, musamman idan kana amfani da shi wajen kira, harkokin banki, ko karbar sakon tabbatarwa na OTP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

A mafi yawan lokuta, matsalar tana da nasaba ne da rashin haɗa layin da lambar katin dan kasa ta NIN, ko kuma akwai wani rashi a bayananan ka.

'Yan Najeriya za su iya dawo da layin MTN da aka rufe sakamakon matsalar NIN
Wasu mutane sun yi cincirindo a ofishin MTN don bude layukansu da aka rufe saboda matsalar NIN. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amma babban dadi anan shi ne, ana iya magance yawancin matsalolin NIN-SIM cikin sauri ba tare da sai ka je cibiyar kula da abokan ciniki ta MTN ba, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Ga matakai masu sauki da za ku bude layin MTN da aka rufe saboda matsalar NIN.

1. Duba matsayin NIN dinka tukuna

Kafin ka fara ko wani kokari, tabbatar ko layin ka na MTN yana da alaka da lambar NIN dinka ta gaskiya.

Kara karanta wannan

Ndume ya musanta zargin shiga tsakani da 'yan bindiga, ya nemi a binciki Kaigama

MTN ta samar da wani shafi na musamman inda masu amfani da layinta za su iya duba halin da layinsu yake ciki ta hanyar shigar da lambar waya tare da tabbatar da hakan ta amfani da OTP.

Idan ba a haɗa layin ka ba ko kuma yana buƙatar karin bincike, shafin zai nuna maka matakan da ya kamata ka dauka.

2. Haɗa NIN dinka idan ba a yi ba

Idan har ba a haɗa lambar NIN dinka da layin MTN ba, ka kammala aikin hakan da zarar zai yiwu. Gwamnatin Tarayya ta ɗora dokar cewa kowane sim din da yake aiki dole ne a haɗa shi da ingantacciyar lambar NIN.

Zaka iya tura lambar NIN dinka ta hanyoyin da MTN ta amince da su, kamar shafin yanar gizon su, manhajar myMTN, ko kuma ta hanyar ziyartar cibiyar kula da abokan ciniki.

Ana kammala rajistar sim ne kawai idan an tabbatar da an haɗa shi da NIN cikin nasara.

3. Tabbatar da bayanan NIN sun yi daidai

Wani lokacin matsalar ba rashin NIN ba ce, a'a, bayanan ne ba su yi daidai ba. Idan suna, ranar haihuwa, ko sauran bayanai a kan rajistar sim din ba su yi daidai da wadanda ke wurin hukumar NIMC ba, tabbatarwa za ta iya faduwa.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Naira tiriliyan 80? Minista ya yi martani

Idan hakan ta faru, zaka iya bukatar gyara bayanan ka a wurin NIMC ko kuma ka je ofishin MTN domin samun taimako.

4. Sake kunna wayarka bayan tabbatarwa

Da zarar an tabbatar da an haɗa NIN dinka tare da yin daidai, layin ka ba zai dawo da aiki ba a take.

Sake kunna wayarka ko kuma ka kunna sannan ka kashe yanayin jirgin sama domin ba wa na'urar ka damar sake shiga sabuwar hanyar sadarwa.

A mafi yawan lokuta, ana dawo da zirga-zirgar kiran waya da sauran ayyuka ba da jimawa ba bayan an kammala tabbatar da bayanan.

An bukaci maso son bude layinsu na MTN da su duba ko suna da bukatar sabunta bayanansu na NIN
Mutane suna zazzaune a ofishin hukumar NiMC inda suke son sabunta bayanansu na NIN. Hoto: Pius Utomi/GettyImages
Source: Getty Images

5. Ziyarci cibiyar MTN idan matsalar ta ci gaba

Idan layin ka ya ki bude wa duk da cewa ka gama haɗa NIN dinka, ka je cibiyar MTN mafi kusa da kai dauke da takardar shaida ta NIN ko Virtual NIN tare da ingantacciyar shaida ta ɗan adam.

Ma'aikatan kula da abokan ciniki na MTN za su iya duba halin da rajistar ka take ciki, su gyara kura-kurai, su kuma taimaka wajen dawo da layin ka idan hakan ta zama dole, kamar yadda rahoton Tech Cabal ya nuna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu tayi maganar yadda za a raba rijiyoyin mai a Najeriya

An sanya wa'adin mallakar NIN

A wani labari, mu ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar NIMC ta tabbatar kowane ɗan Najeriya ya yi rijistar NIN kafin ƙarshen 2026.

Shugabar hukumar NIMC ta kasa, Abisoye Coker-Odusote ta ce tsarin rijistar lambar zama dan kasa ya haramta mallakar NIN guda biyu.

Ta bayyana cewa kammala yi wa kowane dan Najeriya rijistar NIN zai ba da damar sanin jimullar adadin mutanen da kasar ke da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com