Ganduje Ya Tsokano NDC da Obidients, Sun Yi Masa Raddi Mai Zai kan Taba Obi, Kwankwaso

Ganduje Ya Tsokano NDC da Obidients, Sun Yi Masa Raddi Mai Zai kan Taba Obi, Kwankwaso

Jam'iyyar NDC da Obidient Movement sun yi watsi da ikirarin Ganduje kan tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sun bayyana cewa Obi da Kwankwaso na da tarihin shugabanci da magoya baya da za su iya kai su ga nasara a zaɓen 2027

Yunusa Tanko ya kalubalanci Ganduje kan cancantarsa ta yin magana kan tarihin siyasar Obi da Kwankwaso

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Jam'iyyar NDC da Obidient Movement sun yi watsi da ikirarin tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje, cewa tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba shi da tarihin siyasa da zai iya kai shi ga nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sun dage cewa shugabannin biyu na da tarihin shugabanci da kuma dimbin magoya baya da za su iya taimaka musu samun nasara a zaɓe, musamman a Jihar Kano da sauran sassan ƙasar.

Kara karanta wannan

An ji labarin abin da aka tattauna da Peter Obi ya zauna da Jakadan kasar Switzerland

Mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa na NDC, Abdulmumin Abdulsalam, ya bayyana hakan da yake mayar da martani a wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar The Punch.

Me Ganduje ya ce kan Obi, Kwankwaso?

A ranar Talata ne Ganduje ya bayyana tikitin Obi da Kwankwaso a ƙarƙashin inuwar NDC a matsayin wanda ba zai kai labari ba.

Ya bayyana cewa babu daya daga cikin Obi ko Kwankwaso da ke da cancantar shugabanci ko tarihin siyasa da zai ba su damar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wane martani NDC ta yi wa Ganduje?

Da yake mayar da martani, Abdulmumin Abdulsalam ya yi watsi da kalaman Ganduje, yana mai cewa tsohon shugaban APC ya rasa tasirinsa a siyasar Kano.

“Ina ganin Ganduje dai surutu kawai yake yi. Amma mu a NDC mun yi imanin cewa idan muka zo wurin, za mu yi nasara. Haka kuma mun yi imanin cewa siyasa ta dogara ne kan tabbatar da shahararka."

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

“Ganduje a yau ba shi da farin jini a Kano. A gaskiya ma, a cikin jam’iyyarsa an mayar da shi dan kallo, kuma ya fara rasa matsayinsa a jam’iyya mai mulki."
“Ba zai iya kwatanta APC a Jihar Kano da NDC ba. Jam’iyyarmu ba ta taɓa shiga zaɓe a Jihar Kano ba, amma zan iya gaya maka cewa, bisa yadda NDC ta gyara gidanta, za mu ci nasara a Kano a kowane lokaci.”

- Abdulmumin Abdulsalam

Abdulmumin Abdulsalam ya ce jam’iyyar na da kwarin gwiwar lashe kujerun zaɓe a Kano saboda tasirin siyasar Kwankwaso.

Ya kuma ce sakamakon da Obi ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya nuna irin karɓuwarsa a faɗin ƙasar, yana hasashen cewa tsohon gwamnan Anambra zai samu ƙarin kuri’u a 2027.

Obidients ta tankawa Ganduje

Shi ma da yake mayar da martani, shugaban kungiyar Obidient Movement Worldwide, Dr Yunusa Tanko, ya tambayi cancantar Ganduje ta yin magana kan tarihin Obi da Kwankwaso.

“Ban san dalilin da ya sa har yanzu mutane ke ɗaukar Ganduje da muhimmanci ba. Ba shi da cancantar kalubalantar mutumin da ya bar Naira biliyan 75 a asusun gwamnatin Jihar Anambra.” In ji shi

Kara karanta wannan

Kalaman Kwankwaso game da rashin tsaro ya yi wa APC zafi, an yi masa martani

Ganduje ya caccaki Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso martani kan batun tattaunawa da 'yan bindiga.

Ganduje ya ce duk wata yarjejeniya da ake yi da 'yan bindiga tana ba su damar ƙara samun kuɗi da kayan aiki, lamarin da zai ƙara tsananta matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng