Yadda Gwamnatin Marigayi Buhari Ta Kashe N1.16bn na Tallafin Man Fetur

Yadda Gwamnatin Marigayi Buhari Ta Kashe N1.16bn na Tallafin Man Fetur

  • Hukumar RMAFC ta bayyana cewa Najeriya ta kashe tiriliyan ₦1.16 wajen tallafin fetur a 2021, sannan aka cire tiriliyan ₦1.20 daga kudin danyen mai kai tsaye
  • Shugaban RMAFC, Dakta Mohammed Bello Shehu, ya ce asarar mai, gyaran bututun mai da ajiyar man fetur sun kara rage kudaden shiga na tarayya
  • Kwamitin Majalisar Dattawa ya gargadi Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya gurfana ranar Talata ko kuma a dauki matakin tilasta masa halarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Tattara da Raba Kudaden Shiga ta Kasa (RMAFC) ta bayyana cewa Najeriya ta kashe tiriliyan ₦1.16 wajen tallafin man fetur a shekarar 2021.

Haka kuma, an cire karin tiriliyan ₦1.20 kai tsaye daga kudaden da aka samu daga sayar da danyen mai.

Yawan kudi da aka kashe kan tallafin mai a mulkin Buhari
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Shugaban hukumar, Dakta Mohammed Bello Shehu, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja yayin gabatar da bayani gaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Asusun Jama'a, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An tsare tsohon jami'in DSS a gidan kaso kan zargin alaka da kungiyar ta'addanci

Kwamitin, karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Dankwabo mai wakiltar Gombe ta Arewa, na binciken rahotannin tantance harkokin mai da iskar gas na shekarun 2021 zuwa 2023 da Hukumar NEITI ta fitar.

Da yake bayyana yadda aka cire kudade daga kudin danyen mai, Shehu ya ce tallafin man fetur ba shi kadai ne ya rage kudaden shiga ba.

Ya ce asarar danyen mai da kayayyakin mai ta kai biliyan ₦16.20, yayin da gyaran da kula da bututun mai suka ci biliyan ₦22.05. Ya kara da cewa ajiyar man fetur domin bukatar gaggawa ta lakume biliyan ₦6.75.

Shehu ya kuma nuna damuwa kan yadda ake lissafin kaso 13 cikin 100 na kudaden rabon arzikin mai ga jihohin da ake hako mai.

A cewarsa, lissafa wannan kaso bayan an cire wasu kudade daga jimillar kudaden shiga ya saba da manufar tanadin tsarin rabon arziki, cewar Vanguard.

A yayin zaman, kwamitin ya dakatar da sauraron rahoton Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) domin bai wa mambobinsa damar nazarin takardun da hukumar ta gabatar. Ana sa ran shugabannin hukumar za su sake bayyana a mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwastam ta faɗi lokacin da za ta dauki ma'aikata a 2026, ta sauya tsarinta

Sai dai kwamitin ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin halartar Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya, wanda bai halarta ba kuma bai aika da wakili ba.

Sanata Dankwabo ya gargade shi da cewa dole ne ya gurfana gaban kwamitin ranar Talata mai zuwa, in ba haka ba Majalisar za ta yi amfani da ikon kundin tsarin mulki wajen tilasta masa halarta.

Gwamnatin Tinubu za ta zare tallafin lantarki

An ba ku labarin cewa Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana shirin cire tallafin bangaren wutar lantarki a hankali inda za a fara daga shekarar 2027.

Game da karin kudin wuta, ministan ya ce ba za a sami karin kudin wuta ba nan take ga masu amfani da wutar lantarki a yau da kullum.

Ya ce za a cire tallafin ne daki-daki domin tabbatar da cewa ba a hana al'umma amfanin da suke samu ba, tare da daidaita bashin da ake bi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.