Amurka Ta Rasa Soja a Harin Iran, an Saki Hoto da Suna
- An tabbatar da mutuwar Sgt. Angel Rampersad, mai shekara 28, a harin Iran kan sansanin sojojin Amurka da ke Jordan
- Rampersad ta kasance cikin jerin mutanen da ba a san inda suke ba bayan harin kafin daga bisani hukumomi su tabbatar da mutuwarta
- An bayyana ta a matsayin sojan Amurka na uku da ya mutu a harin da aka kai sansanin Muwaffaq Salti a ranar 17 ga Yulin 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Ma’aikatar tsaron ta Amurka ta bayyana Sgt. Angel Rampersad, mai shekara 28, a matsayin soja na uku da ya mutu a harin Iran kan sansanin sojin Muwaffaq Salti da ke Jordan a ranar 17 ga Yulin 2026.
Rampersad ta kasance cikin jerin sojojin da ba a san inda suke ba bayan harin, kafin daga bisani hukumomi su tabbatar da mutuwarta.

Kara karanta wannan
Trump ya ji zafin kisan sojojinsa da Iran ta yi, zai karbi gawarwakinsu a wani biki a Amurka

Source: Twitter
A cewar Fox News, an tura Rampersad zuwa runduna ta farko ta Batalilya ta 57th Air Defense Artillery Regiment, 52d Air Defense Artillery Brigade, 10th Army Air and Missile Defense Command, da ke Ansbach a Jamus.
A can ta yi aiki a matsayin 25U Signal Operations Support Specialist, wato kwararriyar mai bayat da tallafin ayyukan sadarwa.
Ma’aikatar tsaro ta yi alhini
Bayan sanar da mutuwarta, jami’an ma’aikatar tsaro sun mika sakon ta’aziyya ga iyalan sojan da wadanda suke jimamin rasuwarta.
“Muna mika matuƙar ta’aziyyarmu daga zuciya ga iyalanta da duk wadanda ke fuskantar wannan babban rashi da ba za a iya misaltawa ba,” in ji ma’aikatar tsaro
Harin da aka kai sansanin sojin Jordan a ranar 17 ga Yulin 2026 ya kara ta'azzara yakin, inda Iran ta dauki alhakin harin da ya yi sanadin mutuwar akalla sojojin Amurka uku.
Bayan tabbatar da sunan Rampersad, adadin sojojin Amurka da aka tabbatar sun mutu a harin ya kai uku, bayan an riga an bayyana sunayen wasu sojoji biyu.
Rampersad ta kasance cikin rundunar da ta mayar da hankali kan tsaron sama da makamai masu linzami, wani bangare da ya kara samun muhimmanci a sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya a cikin 'yan shekarun nan.
Mamdani ya yi alhini
Magajin garin New York, Mamdani, ya yi alhini a shafinsa na X kan mutuwar Rampersad, wadda ta fito daga Ozone Park.
“Muna alhinin rasuwar Sgt. Angel Rampersad, wadda ta fito daga Ozone Park kuma aka kashe a wani sansanin soji da ke Jordan yayin da take yi wa kasarmu hidima.”

Source: Getty Images
Ya kara da cewa za a tuna da jarumtaka da sadaukarwar Rampersad ba kawai a Queens ba, har ma a dukkan gundumomin birnin New York guda biyar.
“Babbar ta’aziyyata tana tare da iyalanta, masoyanta da duk wadanda wannan babban rashi ya shafa,” in ji shi.
Ya ce ga dimbin mazauna New York, yaƙe-yaƙen da ake yi a kasashen ketare ba su da nisa, domin ana jin tasirinsu a gida.
“Sadaukarwar da sojoji da iyalansu ke yi na ci gaba da tunasar da mu wannan. Za mu ci gaba da gode musu saboda hidimarsu, kuma za mu yi aiki a kowace rana domin girmama wannan hidima,” in ji Mamdani.
Trump ya yi wa Iran barazana
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya yi barazanar lalata gada ko tashar samar da wutar lantarki a duk lokacin da Iran ta kai hari kan jirgi a mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng

