Babbar Magana: Atiku Ya Sake Huro Wuta Sai Tinubu Ya Yi Murabus
- Atiku Abubakar ya ce sabanin bayanan OAGF da CBN kan asusun PFIPC ya fallasa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Ya bukaci a gayyaci Akanta-Janar na Tarayya da Gwamnan CBN su bayyana tare a gaban kwamitin bincike
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce idan Tinubu ya kasa dawo da amincewar jama'a, ya kamata ya nemi afuwa ya kuma yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake yin magana kan badakalar hukumar PFIPC.
Atiku ya ce sabanin bayanan da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF) da Babban Bankin Najeriya (CBN) suka bayar kan bude asusun PFIPC ya fallasa gwamnati.

Source: Twitter
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwar Jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026.
Atiku ya ce shaidar da CBN ya gabatar a gaban Majalisar Wakilai ta saba matuka da bayanin da OAGF ya gabatar a baya.
Ya ce wannan ya jefa gwamnatin Tinubu cikin daya daga cikin manyan rikice-rikicen samun yarda a tarihin dimokuradiyyar Najeriya, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Atiku ya yi suka kan mabambantan bayanai
“Wannan ne inda ake ganin boye-boye ya fara. Wata hukuma ta musanta ba da izinin bude asusun PFIPC tare da zargin cewa an yi jabun takardu. Wata kuma, a gaban wakilan al’ummar Najeriya, ta ce an bude asusun ne bisa umarnin Akanta-Janar bayan an bi ka’idojin da suka dace. Ba zai yiwu bayanan biyu su zama gaskiya ba."
“Idan hukumomin ku biyu masu kula da harkokin kudi da na tsarin hada-hadar kudi suka fito fili suka saba wa juna kan wannan ma’amala guda, babu wani shugaba mai muhimmanci da ke bukatar mai hasashen gaibu domin sanin cewa gwamnatinsa ta fada cikin wata hanyar yaudara da kuma babbar matsalar amincewa."
“Shugaban kasa ba zai ci gaba da kallo daga gefe ba yayin da gwamnatinsa ke wargajewa saboda sabanin bayanai."
“Dole Shugaba Tinubu ya amsa tambaya mai sauki: Wane bayani ya yarda da shi, na Akanta-Janar ko na Babban Bankin? Idan bai yarda da ko daya ba, me ya sa bai dauki mataki ba?"
“Duk ranar da ya kara jinkirta ba da umarnin gudanar da bincike na hakika mai zaman kansa, yana kara zurfafa zargin jama’a cewa kare martabar gwamnatinsa ya fi kafa gaskiya muhimmanci a wajensa.”
- Atiku Abubakar

Source: Facebook
Ya bukaci Tinubu ya nema afuwa ya kuma yi murabus
Atiku ya ce 'yan Najeriya na bin Shugaba Tinubu bashin ban hakuri saboda jagorantar abin da ya kira rugujewar tsarin ba da amsa ga jama’a da ba a taba ganin irinsa ba.
Ya ce idan shugaban kasar ba zai iya dawo da amincewar jama’a nan take ta hanyar gudanar da bincike na gaskiya mai zaman kansa tare da tabbatar da cewa duk wadanda ke da hannu sun fuskanci hukunci ba, to ya rasa ikon ci gaba da zama a kan mulki.
“Abin da ya dace abu ne mai sauki: ya nemi afuwar ‘yan Najeriya sannan ya yi murabus.”
- Atiku Abubakar
Atiku ya bukaci Tinubu ya hakura da takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar mai takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2027, ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta shekarar 2027.
Asali: Legit.ng


