Cikakken Jerin Kasashe 44 da 'Yan Najeriya Za Su iya zuwa ba Tare da Biza ba
- Fasfon Najeriya ya sauka zuwa matsayi na 90 a sabon jadawalin Henley Passport Index, amma har yanzu yana ba da damar shiga kasashe 44
- Najeriya ta samu maki 44 na shiga kasashe ba tare da neman biza tun kafin tafiya ba, ciki har da kasashen Afirka da yankin Caribbean
- Masana sun bukaci matafiya su tabbatar da sharuddan shigar kowace kasa, domin wasu na bayar da visa bayan isa ko e-visa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Fasfon Najeriya ya sauka zuwa matsayi na 90 a sabon jadawalin Henley Passport Index na watan Yulin 2026, amma har yanzu masu rike da shi na iya shiga kasashe 44 ba tare da samun biza kafin tafiya ba.
Sabon rahoton da Henley & Partners ta fitar ranar Talata ya nuna cewa fasfon Najeriya ya samu maki 44 na shiga kasashe ba tare da neman biza tun kafin tafiya ba.

Source: Getty Images
Darajar fasfon Najeriya ya sauka
Jadawalin Henley Passport Index na tantance fasfofi 199 bisa yawan kasashen da masu rike da su za su iya shiga ba tare da biza ba, ta amfani da bayanan Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA).
Najeriya ta kasance a matsayi na 90 a duniya, bayan ta sauko daga matsayi na 89 da ta kasance a rahoton watan Afrilu na shekarar 2026.
Sai dai duk da wannan sauyin matsayi, makinta na shiga kasashe 44 bai canza ba.
Rahoton ya kuma nuna cewa Najeriya ta samu ci gaba idan aka kwatanta da shekarar 2025 da ta kasance a matsayi na 94 da kuma shekarar 2021 lokacin da ta kasance a matsayi na 103.
Kasashen da 'yan Najeriya za su iya shiga
Rahoton ya ce masu fasfon Najeriya na iya shiga wadannan kasashe ba tare da biza kafin tafiya ba, ko kuma su samu biza bayan isa ko e-visa:
- Barbados
- Benin
- Burkina Faso
- Burundi (biza bayan isa)
- Cambodia (biza bayan isa)
- Cameroon
- Cape Verde
- Chadi
- Comoros (biza bayan isa)
- Cook Islands
- Côte d’Ivoire
- Djibouti
- Dominica
- Fiji
- Ghana
- Guinea
- Guinea-Bissau
- Haiti
- Iran (biza bayan isa)
- Kenya
- Kiribati
- Lebanon
- Liberia
- Madagascar (biza bayan isa)
- Maldives (biza bayan isa)
- Mali
- Mauritius
- Micronesia
- Montserrat
- Mozambique
- Nijar
- Niue (biza bayan isa)
- Palau Islands (biza bayan isa)
- Rwanda
- Samoa (biza bayan isa)
- Senegal
- Seychelles
- Sierra Leone
- St. Kitts and Nevis
- Gambia
- Timor-Leste (biza bayan isa)
- Togo
- Tuvalu
- Vanuatu

Source: UGC
An gargadi matafiya
Rahoton ya bayyana cewa ba dukkan kasashen ke ba da cikakkiyar shiga ba tare da biza ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wasu kasashen na bayar da biza bayan isa, yayin da wasu ke bukatar matafiya su nemi e-visa kafin tafiya.
Saboda haka, an shawarci 'yan Najeriya da su tabbatar da sabbin sharuddan shige da fice na kasar da suke son ziyarta kafin su shirya tafiya.
Yadda ake sabunta fasfon Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar NIS ta fitar da sabon tsarin sabunta fasfo ga 'yan Najeriya mazauna kasashen waje ta hanyar kai-da-kai ba tare da zuwa ofishin jakadanci ba.
Sabon tsarin ya bai wa masu cancanta damar yin rajistar bayanan tantance su ta manhajar da hukumar ta samar, kuma za su hakan cikin sauki.
Hukumar ta ce wadanda ba su cancanci amfani da tsarin ba ne kawai za su ci gaba da yin rajistar ganawar kai tsaye a ofisoshin jakadancin Najeriya.
Asali: Legit.ng

