Manyan Labarai A Yau
Kungiyar SERAP ta bai wa hukumar INEC wa’adin kwana bakwai ta yi bayani kan yadda aka kashe sama da Naira biliyan 126 da aka ware wa harkokin zaɓe.
Ƙungiyar ’yan siyasar kabilar Igbo a jihohin Arewa 19 da Abuja ta amince da Shugaba Bola Tinubu a 2027, tare da alkawarin samo masa ƙuri’u miliyan biyu.
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gargadi shugabannin Musulmi da Kirista a Osun kan zargin shirin ’yan ta’adda na kai hari wuraren ibada kafin zaɓen 2027.
Al’ummar Musulmin Najeriya a Ireland sun sanar da rasuwar Imam Abdul-Ganiy Adeleke Asubiaro, wanda ya taka rawa wajen ci gaban Musulunci a ƙasar.
Saudiyya ta rufe wani muhimmin bututun mai bayan jiragen marasa matuka daga Iraq sun kai masa hari, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara barazana ga makamashi
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a jihar kan rasuwar Bamanga Tukur, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola.
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar dattijon ƙasa, fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Bamanga Tukur.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar zaɓen shugaban ƙasa na karshe da za su gwabza a zaben 2027.
Tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Bamanga Muhammad Tukur, ya rasu yana da shekara 91, bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari