Tura Ta Kai Bango: Matawalle Ya ba Sojoji Sabon Umarni kan 'Yan Ta'adda
- Karamin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba dakarun Operation Fansan Yamma da sauran rundunonin soji da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma sabon umarni
- Matawalle ya bayar da umarnin ne yayin da yake jajanta wa waɗanda hare-haren 'yan ta'adda na baya-bayan nan suka shafa a Bungudu da sauran al'ummomin Zamfara
- Ministan ya umarci sojoji da su ƙara sanya ido da sintiri domin gano maboyar 'yan ta'adda tare da lalata su kafin su sake amfani da su wajen kai hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Zamfara - Karamin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya umarci dakarun Operation Fansan Yamma da sauran rundunonin soji da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma da su ƙara tsananta farmaki kan 'yan ta'adda bayan sabbin hare-haren da aka kai a wasu sassan Jihar Zamfara
Matawalle ya bayar da umarnin ne yayin da yake jajanta wa waɗanda hare-haren 'yan ta'adda na baya-bayan nan suka shafa a Bungudu da sauran al'ummomin da abin ya shafa a Zamfara, inda ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya na dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan yaɗa labarai, Ahmed Dan Wudil, ya fitar.
A cikin sanarwar, Ministan ya bayyana hare-haren a matsayin abin takaici, tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa jami'an tsaro za su ci gaba da yaƙin da suke yi da 'yan ta'adda.
Matawalle ya bukaci kara zafafa yaƙi
Ya umarci shugabancin Operation Fansan Yamma da su ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ta'addanci tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Ministan ya kuma umarci dukkan rundunonin soji da ke gudanar da ayyukan yaƙi da ta'addanci a Zamfara, Kebbi, Katsina, Sokoto da Kaduna da su ƙara zafafa ayyukansu ta hanyar amfani da dukkan matakan da doka ta amince da su kuma suka dace domin tarwatsa hanyoyin sadarwa da cibiyoyin 'yan ta'adda, ta hanyar abin da ya kira “farmakin musamman ba tare da sassauci ba”
Matawalle ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin al'umma da mazauna yankunan da su taimaka wa hukumomin tsaro da sahihan bayanan sirri cikin lokaci, musamman kan mutanen da ake zargi da taimaka wa 'yan ta'adda da bayanai ko kayan aiki da suke amfani da su wajen shirya hare-hare kan al'ummomin karkara
Ya umarci manyan kwamandojin soji da ke yankunan da ayyukan ta'addanci suka fi tsanani da su ƙarfafa sa ido tare da ƙara sintiri domin gano tare da lalata maboyar 'yan ta'adda da wuraren fakewarsu kafin su yi amfani da su wajen ƙaddamar da wasu hare-hare
An yaba wa jami'an tsaro
Ministan ya yaba wa Rundunar Sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro kan jarumtakarsu, ƙwarewarsu da sadaukarwar da suke yi a yakin da ake ci gaba da yi da ta'addanci
Ya yaba wa dakarun musamman kan ayyukan baya-bayan nan da suka kai ga kashe wasu 'yan ta'adda a Gummi, Bukkuyum, Anka da Tsafe a Jihar Zamfara, da kuma Faskari a Jihar Katsina da sauran wurare.
Matawalle ya bukaci dakarun da su ci gaba da wannan ƙoƙari har sai an fatattaki ta'addanci gaba ɗaya a sassan ƙasar da abin ya shafa
Ya kuma yi addu'ar Allah Ya ci gaba da ba sojoji da sauran hukumomin tsaro nasara a ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
Matawalle ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa Bello Matawalle, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
Karamin Ministan tsaron ya bayyana cewa Allah ne kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
Asali: Legit.ng


