An Bayyana yadda Yariman Saudiyya Abdullah bin Fahad Ya Rasu a Otal din Landan
- Bincike ya bayyana cewa Yarima Abdullah bin Fahad ya mutu ne sakamakon bugun zuciya bayan haɗa barasa, kwayar GHB da wasu kwayoyi
- Rahoton ya nuna cewa marigayin ya taba samun jinya domin daina shan barasa da magunguna a cibiyoyin Priory da Rainford Hall kafin rasuwarsa
- Kotun da ke binciken ta ce babu wata shaida da ke nuna ya kashe kansa ko wani ya shiga lamarin, bayanan CCTV sun nuna yana shi kadai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Landan - Kotun bincike da ke birnin Landan ta bayyana cewa wani dan gidan sarautar Saudiyya, Yarima Abdullah bin Fahad bin Abdullah bin Abdulaziz bin Jalawi Al Saud, ya mutu ne sakamakon bugun zuciya bayan haɗa barasa da kwayar GHB tare da wasu magungunan rage damuwa.
An gano gawar yariman mai shekara 29 a makewayin dakinsa da ke otel din Marriott da ke Kensington, yammacin Landan, a ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

Source: Twitter
Yadda aka gano gawar Yarima a otel
Kotun binciken mutuwa ta Inner West London Coroner’s Court ta ji cewa marigayin ya shiga otel din ne a ranar 19 ga Nuwamba domin yin zama na mako guda, in ji rahoton The Independent.
Rahotanni sun nuna cewa na'urar CCTV ta kama shi a karo na karshe da yammacin ranar da ta gabaci rasuwarsa lokacin da ya fita wajen shan taba sigari.
Sai dai washegari, wani ma'aikacin tsaftace otel ya shiga dakinsa bayan an bude kofar da aka kulle, inda ya tarar da shi kwance a kasa cikin bandaki yana sanye da tufafinsa.
An kira jami'an tsaron otel da ma'aikatan gaggawa, amma duk kokarin farfado da shi bai yi nasara ba, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Yadda barasa da kwayoyi suka yi ajalinsa
Rahoton gwajin sinadarai ya nuna cewa yawan barasar da ke cikin jininsa ya kai milligram 222 cikin millilita 100 na jini, wanda ya zarce iyakar da doka ta tanada ga masu tuki da kusan sau uku.
Haka kuma, an gano adadin kwayar GHB da ake kira “party drug” a jikinsa, tare da ragowar tabar wiwi da maganin rage damuwa na Xanax da wasu magunguna.
Rahoton jaridar The Times ya nuna cewa binciken gawa ya tabbatar da cewa bugun zuciya ne ya kashe yariman bayan haɗuwar wadannan sinadarai a jikinsa.
Ya taba zuwa cibiyoyin jinyar shaye-shaye
Kotun ta kuma ji cewa marigayin ya dade yana fama da matsalar shan barasa da Xanax.
A watan Agustan shekarar da ta gabata ya yi jinya a cibiyar Priory Clinic da ke Roehampton, cibiyar da ta shahara wajen kula da masu fama da shaye-shaye.
Likitar kwakwalwa, Dr Victoria Chamorro, ta bayyana cewa marigayin ya hada kai sosai yayin jinyarsa kuma ya kammala shirin cire masa barasa da magungunan da yake sha ba tare da wata matsala ta lafiya ba.
Bayan ya bar Priory, ya sake samun kulawa a cibiyar Rainford Hall da ke St Helens, inda daga baya aka sallame shi bayan ya murmure daga wata cutar hanyoyin numfashi.

Source: Twitter
Kotun ta ce ba ya da niyyar kashe kansa
Mai taimaka wa coroner, Jean Harkin, ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa yariman ya kashe kansa.
Ta bayyana cewa rahotannin cibiyoyin jinyar da ya taba zuwa sun nuna babu wata alamar cewa yana da niyyar kashe kansa, kuma ba a samu wata takardar ban kwana a dakinsa ba.
Kotun ta kuma ce babu wata shaida da ke nuna wani ya shiga lamarin, domin hotunan CCTV sun nuna cewa marigayin yana shi kadai a daren da ya gabaci rasuwarsa.
Yarima mai doguwar suma ya rasu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Yarima Al-Waleed bin Khaled ya rasu bayan shekaru 20 cikin dogon suma da ya faru bayan hatsarin mota a London.
An ajiye marigayin tun shekaru 20 da suka wuce watau 2005 bayan mummunan haɗarin mota da ya gamu da ita.
Yariman ya samu haɗarin ne a London yana karatu a makarantar soja, inda rauni ya jawo masa zubar jini a kwakwalwa.
Asali: Legit.ng


