Shugaba Tinubu Ya Kwantar da Hankulan 'Yan Arewa kan Matsalar Rashin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Kwantar da Hankulan 'Yan Arewa kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalolin tsaro da ke addabar Arewa da sauran sassan Najeriya za su zama tarihi nan ba da jimawa ba
  • Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri domin kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin ƙasar
  • Manyan gwamnonin Arewa da wasu tsofaffin shugabannin yankin ba su halarci taron tunawa da Janar Hassan Usman Katsina ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalolin tsaro da ke addabar Arewa da sauran sassan Najeriya za su zama tarihi nan ba da jimawa ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri domin kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka a ƙasar.

Tinubu ya yi magana kan rashin tsaro
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa a taron tunawa da Janar Hassan Usman Katsina karo na uku da aka gudanar a Kaduna.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware minista 1 a cikin mukarrabansa, musamman ya koda shi

Shugaban ƙasan, wanda hadiminsa na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Masari, ya wakilta, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta kare abubuwan tarihi da kyawawan ayyukan jaruman da suka gabata.

Tinubu ya yaba wa Hassan Usman Katsina

Shugaba Tinubu ya ce marigayi Janar Hassan Usman Katsina ya yi wa ƙasa hidima ta musamman, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Yayin da yake karrama marigayin, shugaban ƙasan ya bayyana shi a matsayin abin koyi na tawali'u, ladabtarwa, kishin ƙasa da sadaukar da kai wajen yi wa jama'a hidima.

Ya ce tsohon gwamnan soji na tsohuwar Arewacin Najeriya, wanda daga baya ya zama babban hafsan sojin ƙasa, ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta haɗin kan ƙasa da ƙarfafa Najeriya a wasu muhimman lokuta na tarihinta.

“Janar Hassan Usman Katsina ya kasance abin koyi wajen kyawawan halayen hidimar jama'a, tawali'u, jarumtaka, ladabtarwa da ƙaunar Najeriya marar iyaka. Ya kasance ɗan Arewa nagari kuma ɗan ƙasa nagari."
"Koƙarinsa na musamman wajen tabbatar da haɗin kan ƙasar nan ya taimaka wajen kafa wani ɓangare na ginshiƙan dimokuraɗiyya da 'yancin da muke morewa a yau."

Kara karanta wannan

"Arewa ta rasa ƙimarta," Farfesa Ango Abdullahi ya yi maganganu masu zafi

“Domin tarihi ya nuna, Janar Hassan Usman Katsina ya yi wa ƙasarmu hidima ta musamman. A matsayinsa na gwamnan soji na tsohuwar Arewacin Najeriya, sannan daga baya babban hafsan sojin ƙasa a lokacin Yaƙin Basasa, ya nuna jarumtaka, kishin ƙasa da hangen nesa na musamman."
"Baya ga matsayi da mukami, ya rayu ne domin amfanin jama'a baki ɗaya. Ya yi imani da ilimi, mutunci da darajar kowane ɗan Najeriya. Waɗannan su ne ƙimomin da ya kamata su ci gaba da jagorantar mu,” in ji Tinubu
Tinubu ya ce za a kawo karshen rashin tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Matsalar tsaro za ta wuce

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na aiki dare da rana domin tabbatar da tsaron ƙasar.

“Yayin da muke ci gaba da aiki dare da rana domin tabbatar da tsaron ƙasarmu, da ikon Allah, matsalolin rashin tsaron da muke fuskanta, musamman a Arewacin Najeriya, nan ba da jimawa ba za su zama tarihi,” in ji shi

Abin da ya jefa Arewa a matsala

A wani labarin kuma, kun ji cewa Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana cewa babban abin da ya jefa Arewa cikin matsalolin da take fama da su a yau shi ne rasa kyawawan ƙimomi da magabata suka gada.

Farfesa Ango ya ce yankin ya kauce daga turbar shugabanni na farko waɗanda suka gina Arewa bisa gaskiya, adalci, sadaukarwa da shugabanci nagari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng