Kalaman Mai Neman Takarar Gwamna a APC Sun Ja an Gurfanar da Ita gaban Kotu

Kalaman Mai Neman Takarar Gwamna a APC Sun Ja an Gurfanar da Ita gaban Kotu

  • An gurfanar da mai neman takarar kujerar gwamnan Ekiti a inuwar APC kan zargin wallafa saƙonnin da ba a ba ta izini ba da kuma tura saƙonnin barazana
  • An zarge ta da wallafa hotuna da adireshin Adeleke Ajibade da Okewale Olayemi tare da saƙonnin barazana
  • Kotun ta bayar da belinta bisa amincewar kanta tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuli, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Ado-Ekiti - An gurfanar da wata mai neman takarar kujerar gwamnan Jihar Ekiti a jam’iyyar APC, Mrs. Abimbola Olajumoke Olawumi, a gaban Kotun Majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti kan.

An gurfanar da ita ne kan zargin tura saƙonnin da ba a ba ta izini ba a kafafen sada zumunta da kuma aika saƙonnin barazana.

Kara karanta wannan

Baya ta haihu, masu neman takara a APC sun nemi a mayar masu kudinsu

An kai yar takarar gwamnan APC a kotu
Abimbola ta gurfana gaban kotu Hoto: Olayinka Damilola
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton zaman shari'ar a ranar Juma'a, 24 ga watan Yulin shekarar 2026.

An kai karar mai neman takara a APC

Mai gabatar da ƙara kuma jami’in shari’a, S. O. Osobu, ya shaida wa kotun cewa a watan Maris na 2026, wadda ake tuhuma ta tura saƙonnin da ba a ba ta izini ba da gangan a kafafen sada zumunta, musamman Facebook da TikTok.

An zarge ta da wallafa hotuna da adireshin Adeleke Ajibade da Okewale Olayemi tare da saƙonnin barazana.

Osobu ya ƙara da cewa wadda ake tuhuma ta kuma wallafa hotunan Mrs. Yemisi Samuel Joluwe (YSJ) tare da saƙon barazana, inda ta zarge ta da karkatar da kuɗaɗen Gwamnatin Jihar Ekiti ba tare da bayar da wata hujja ba.

Wadanne laifuka ake zarginta da su?

A cewar jami’in shari’ar, laifukan da ake zargin ta da aikatawa sun saba wa Sashe na 398 da na 106 na Dokar Laifuka ta Jihar Ekiti ta shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana bayan ganin kumfa a Kaduna

Lauyoyin wadda ake tuhuma, A. O. Okunola, O. G. Abiola da T. E. Akinwumi, sun roƙi kotun da ta bayar da belinta bisa sanayya, inda suka tabbatar da cewa ba za ta tsere daga beli ba kuma za ta kasance a shirye domin fuskantar shari’ar.

Okunola ya bayyana cewa Olawumi tsohuwa ce kuma fitacciyar ‘yar takarar kujerar gwamnan jihar a zaɓen fidda gwani na APC na shekarar 2026.

Babban Majistare, Mr. Abayomi Adeosun, ya bayar da belin Olawumi bisa sanayya tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuli, 2026.

Olawumi ta yi zargin an sace ta

Da take magana da manema labarai bayan zaman kotun, Mrs. Olawumi ta yi Allah-wadai da zargin sace ta da aka yi a ranar Laraba a Abuja.

Ta ce a lokacin da take fita daga Kotun Ƙoli domin karɓar Certified True Copy (CTC) da kotun ta buƙata, jami’an Rapid Response Squad (RRS) suka tare ta, suka tilasta mata shiga motarsu sannan suka kawo ta Ado-Ekiti a daren Laraba.

Ta yi zargin cewa Gwamnatin Jihar Ekiti tana amfani da Mrs. Joluwe wajen tsoratar da ita, inda ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani tare da kare ta da iyalanta daga ci gaba da tsangwama.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi babban kamu a Borno, sun cafke ɗan kasar waje dake tallafawa ISWAP

An gurfanar da mai neman takarar gwamna a APC
Taswirar jihar Ekiti, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A wani ƙarin bayani da lauyoyinta suka yi, sun ce a halin yanzu akwai wasu shari’o’i biyu da ke gudana kan lamarin, ciki har da binciken da Ofishin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP) ke gudanarwa.

Lauyoyin sun kuma yi zargin cewa shari’ar na da alamun siyasa karara.

Shugaban APC ya ba da shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ba shugabannin 'yan adawa shawara.

Farfesa Nentawe ya bukaci su mayar da hankali wajen gabatar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com