Obasanjo Ya Fallasa Yadda Atiku Ya Kitsa Yunkurin Tsige Shi daga Mulki

Obasanjo Ya Fallasa Yadda Atiku Ya Kitsa Yunkurin Tsige Shi daga Mulki

  • Olusegun Obasanjo ya zargi tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar da ba marigayi Ghali Na’Abba N5m domin fara yunkurin tsige shi
  • Tsohon shugaban kasar ya ce yunkurin tsige shi ya samo asali ne daga cikin fadar shugaban kasa a wa’adinsa na farko
  • Atiku da Obasanjo sun yi aiki tare a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa daga shekarar 1999 zuwa 2007

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zargi tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, da kitsa yunkurin tsige shi daga kan mulki.

Obasanjo ya zargi Atiku da bayar da N5m ga tsohon shugaban majalisar wakilai, marigayi Ghali Na’Abba, domin fara yunkurin tsige shi a wa’adinsa na farko.

Obasanjo ya yi zarge-zarge kan Atiku
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar Hoto: Alex C Otti, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba, game da abubuwan siyasa da suka faru kafin babban zaben 2003, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya tsame kansa kan zargin kifar da tsohon gwamna, ya saka sunan Atiku

Yadda aka yi yunkurin tsige Obasanjo

A cikin wata sanarwa, tsohon shugaban kasar ya ce yunkurin tsige shi ya samo asali ne daga cikin fadar shugaban kasa, inda Atiku ya jagorance shi bayan wata ganawa ta sirri da Na’Abba, TheCable ta kawo labarin.

A cewar Obasanjo, Atiku ya shawo kan marigayi kakakin majalisar cewa ya kamata ya yi wa’adi guda kacal a matsayin shugaban kasa, sannan ya karfafa masa gwiwar fara shirin tsige shi.

“Yunkurin tsige Na’Abba ya fara ne daga fadar shugaban kasa ta hannun mataimakin shugaban kasa, wanda a ranar Juma’a, lokacin da ba na ofis, ya gayyaci Na’Abba zuwa ofishinsa kuma ya shawo kansa, kamar yadda ya shawo kan kansa da wasu kadan daga cikin mutane, cewa ya kamata na yi wa’adi guda kacal a matsayin shugaban kasa,” in ji Obasanjo.

Obasanjo ya ce Atiku ya ba da N5m

Obasanjo ya kara zargin cewa Atiku ya bayar da kudin fara yunkurin tsige shi.

Kara karanta wannan

"Da an kai shi gidan yari"; Fadar shugaban kasa ta jikawa Atiku aiki kan taba Tinubu

“Ranar Juma’a, Atiku ya gayyaci Na’Abba; ya ba shi N5m domin ya fara aikin tsige ni. An rubuta komai, an adana bayanansa kuma an kawo mini rahoto ta hannun shugaban ma’aikata na, wanda kwararren jami’in leken asiri ne,” in ji shi.

Tsohon shugaban kasar ya dage cewa an rubuta bayanan ganawar da ake zargin an yi da kuma batun kudin, sannan shugaban ma’aikatansa ya kawo masa bayanan.

Duk da zargin shirin tsige shi, Obasanjo ya ce bai damu da barazanar ba saboda ya yi amanna cewa babu wani dalili na kundin tsarin mulki da zai ba da damar cire shi daga mukaminsa.

Obasanjo ya yi zargi kan Atiku
Olusegun Obasanjo tare da Rabiu Kwankwaso a fadar sarkin Kano Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Dambarwar Atiku da Obasanjo

Sabon zargin ya kara wani babi cikin doguwar hamayyar siyasa tsakanin Obasanjo da Atiku, wadanda dangantakarsu ta ci gaba da kasancewa cikin rashin jituwa tun bayan da suka yi wa’adi tare daga 1999 zuwa 2007.

A lokacin da ake hada wannan rahoto, Atiku bai mayar da martani kan zargin da Obasanjo ya yi ba.

Maganar Obasanjo kan yakin basasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta iya sake fuskantar wani yaƙin basasa ba.

Obasanjo ya bayyana cewa har yanzu da dama daga cikin abubuwan da suka haddasa yaƙin basasar 1967 zuwa 1970 suna nan ba a magance su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng