"Ina da Hujja": Al Mustapha Ya Yi Magana kan Batun Rasuwar Janar Abacha

"Ina da Hujja": Al Mustapha Ya Yi Magana kan Batun Rasuwar Janar Abacha

  • Tsohon babban jami'in tsaron marigayi Janar Sani Abacha ya yi watsi da ikirarin Dennis Amachree kan lokutan karshe na tsohon shugaban mulkin soja
  • Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) ya ce labarin karya ne tare da kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da shi
  • Ya ce yana da faifan CCTV da ke nuna abin da ya faru, amma bai bayyana ko zai fitar da su ga jama'a ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon babban jami'in tsaron marigayi shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya yi watsi da ikirarin wani tsohon jami'in Hukumar DSS, Dennis Amachree, kan lokutan karshe na marigayin.

Al-Mustapha ya bayyana labarin a matsayin karya tare da kira ga 'yan Najeriya da kada su yarda da shi.

Kara karanta wannan

Tsaro: Tsohon daraktan DSS ta dura kan Pantami, ya faɗi illar naɗa shi minista

Al-Mustapha ya yi magana kan mutuwar Abacha
Manjo Hamza Al-Mustapha zaune a wajen taro Hoto: Dr Hamza Al Mustapha
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce ya yi wannan magana ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen taron tunawa da Janar Hassan Usman Katsina karo na uku, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna ranar Asabar, 25 ga watan Yulin 2026.

Martanin nasa ya biyo bayan maganganun da ake yi kan littafin Amachree mai suna The Shadow Warrior, inda rahotanni suka ce tsohon jami'in DSS din ya bayyana nasa bayanin kan abubuwan da suka faru da suka shafi mutuwar Abacha a ranar 8 ga Yuni, 1998.

Al-Mustapha ya karyata Ikirarin

Da yake watsi da ikirarin, Al-Mustapha ya zargi marubucin da kirkirar labarin, yana mai cewa bai yi daidai da abin da ya faru ba.

“Wasu ne suka bukaci yaron ya rubuta wadannan karyace-karyacen. Ina da dukkan faifan CCTV na abin da ya faru a hannuna, don haka abin da ya fada ba gaskiya ba ne,” in ji Al-Mustapha

Kara karanta wannan

Jigon ADC: 'Hari kan mahaifar mataimakin gwamna ya nuna ba mafaka a Sokoto'

Tsohon sojan ya dage cewa yana da hujjojin da za su karyata bayanin abubuwan da suka faru da aka wallafa a cikin littafin, amma bai yi karin bayani kan faifan ba ko kuma ya nuna ko yana da niyyar fitar da su ga jama'a.

Ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin, yana mai cewa ba daidai ba ne a yi zargin wani mamaci da ba zai iya kare kansa ba, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

“Ku yi watsi da karyarsa kawai. Ba daidai ba ne a fadi irin wadannan abubuwa kan mutumin da ya mutu,” in ji shi
Al Mustapha ya ce yana da hujja kan mutuwar Abacha
Tsohon babban dogarin Janar Abacha, Hamza Al-Mustapha Hoto: Dr. Hamza Al-Mustapha
Source: Facebook

Abin da ya faru da Abacha

Abacha, wanda ya karbi mulki ta hanyar juyin mulkin soja a ranar 17 ga Nuwamba, 1993, ya mulki Najeriya har zuwa rasuwarsa kwatsam a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar 8 ga Yuni, 1998.

A lokacin, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa shugaban mulkin kasar ya mutu ne bayan fama da wata rashin lafiya, amma yanayin da ya dabaibaye rasuwarsa ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin abubuwan da suka fi janyo ce-ce-ku-ce a tarihin siyasar Najeriya.

Al Mustapha zai fito takara

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon babban dogarin tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, watau Manjo Hamza Al-Mustapha zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya jaddada kudurinsa na yi wa Najeriya hidima da kuma dawo da martabarta a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng