Gwamnatin Bauchi Ta Kayyade N1,500 a Matsayin Sadaki? An Ji Gaskiyar Zance

Gwamnatin Bauchi Ta Kayyade N1,500 a Matsayin Sadaki? An Ji Gaskiyar Zance

  • Gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta yi magana kan tsayayyen sadakin Naira 1,500 ga matan da aka saki ba
  • An dai yada cewa gwamnati ta kayyade sadakin da za a rika biya domin auren zawarawa da matan da suka dade ba su yi aire
  • Kwamishina Muhammad Binni ne ya yi magana kan bidiyon da ke yawo a Facebook da TikTok wanda ke bayyana kayyade sadakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi ta karyata wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa Gwamna Bala Mohammed ya amince da tsayayyen sadakin Naira 1,500 ga matan da aka saki.

Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, mai yaudarar jama'a da kuma wani yunkuri na ganganci na yaɗa bayanan da ba su dace ba.

Kara karanta wannan

"Ina da hujja": Al Mustapha ya yi magana kan batun rasuwar Janar Abacha

An ce an kayyade sadaki a Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Source: UGC

Kwamishinan Harkokin Addini da Sauya Dabi'un Al'umma, Muhammad Binni, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labatai jawabi a Bauchi ranar Lahadi, 26 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton The Punch.

Binni ya ce bidiyon da ke yawo a Facebook da TikTok ya kuma yi ƙaryar cewa sarkin gargajiya na Zar (Gum Zar) ya umarci mazauna yankin su bi wannan sabon tsarin da aka danganta ga gwamnatin jihar.

Ya bayyana zargin a matsayin “ƙarya ce tsagwaronta, marar tushe kuma kirkirarra”, jatidar Leadership ta kawo labarin.

Gwamnati ta musanta batun sadaki

Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar Bauchi ba ta taɓa fitar da wata doka ko umarni da ya shafi sadakin matan da aka saki ko matan da ba su yi aure ba.

"Gwamnatin Jihar Bauchi ba ta taɓa fitar da wata doka ko umarni da ya shafi sadakin matan da aka saki ko matan da ba su yi aure ba. Bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙarya ne kuma an ƙirƙire su ne domin yaudarar jama'a.” In ji shi

Kara karanta wannan

Tsaro: Tsohon daraktan DSS ta dura kan Pantami, ya faɗi illar naɗa shi minista

Ya bukaci mazauna jihar da su yi watsi da bidiyon tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tantance ba, waɗanda ka iya jawo tashin hankali da rikice-rikice ba tare da dalili ba.

“Muna kira ga jama'a da su yi watsi da bidiyon da ke yawo tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tantance ba, waɗanda ka iya jawo tashin hankali da rikice-rikice ba tare da dalili ba.” In ji shi
Gwamnati ta musanta kayyade sadaki a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnati ta kare al'adun Bauchi

Kwamishinan ya ƙara da cewa Gwamna Bala Mohammed ya ci gaba da mutunta akidun addini, dabi'un al'adu da kuma al'adun mutanen Jihar Bauchi tun bayan da ya hau mulki.

Binni ya kuma yi kira ga jama'a da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su a kafafen sada zumunta.

Wani dan Bauchi, Mukhtar Aliyu Yelwan Kagadama da muka tattauna da shi, ya ce ko da suka ga labarin sun yi mamaki, yana mai cewa:

"Wallahi ni ina gani na san cewa wannan sharrin 'yan midiya ne, ta ya za a ce gwamna ya kayyade sadakin aure, kuma wai N1,500, haba dai, ai abin kana ji ka san babu tsari."

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Wata bazawara da muka tattauna da ita kan yadda suka ji wannan labari, Lantana Basiru Anguwan Ngass, ta ce sun yi mamaki sosai.

"Ni ina zaune ne sai wani yake tura mun labarin ta WhatsApp, wai an mayar da sadakin wadanda auren su ya mutu zuwa N1,500 a Bauchi, sai abin ya bani mamaki.
"Watau har darajar mu ta fadi kasa sosai da sadakinmu zai koma N1,500? Ai ko goma ta lalace, ta fi biyar albarka. To amma yanzu da ka fada mun cewa ba gaskiya ba ne, sai na dan ji sanyi, don har na shirya hawa tiktok in yi martani."

- Lantana Basiru Anguwan Ngass.

Gwamnan Bauchi ya yi garambawul

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amince da yin ƙaramin garambawul a majalisar zartarwar jihar.

Gwamna Bala ya sauke kwamishinoni biyu daga mukamansu, sannan ya amince da murabus na wani kwamishina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng