"Arewa Ta Rasa Ƙimarta," Farfesa Ango Abdullahi Ya Yi Maganganu Masu Zafi
- Farfesa Ango Abdullahi ya ce rasa ƙimomin da magabata suka gada ne ya jefa Arewa cikin matsalolin talauci, rashin tsaro da durƙushewar shugabanci
- Shi ma Farfesa Usman Bugaje ya ce shugabannin Arewa sun kauce daga tafarkin gaskiya da sadaukarwar Janar Hassan Katsina, abin da ya jawo koma baya
- Dattawan sun bukaci shugabannin Arewa su rungumi gaskiya, adalci da hidimar al'umma domin dawo da ci gaba da martabar yankin baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Kaduna - Fitaccen dattijon Arewa kuma tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello (ABU), Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana cewa babban abin da ya jefa Arewa cikin matsalolin da take fama da su a yau shi ne rasa kyawawan ƙimomi da magabata suka gada.
Ya ce yankin ya kauce daga turbar shugabanni na farko waɗanda suka gina Arewa bisa gaskiya, adalci, sadaukarwa da shugabanci nagari.

Source: Facebook
Ango Abdullahi ya fadi matsalolin Arewa
Farfesan ya bayyana hakan ne yayin taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku da aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna, in ji rahoton Daily Trust.
Taron ya mayar da hankali kan yadda za a dawo da kyawawan manufofin marigayin domin bunƙasa Arewa.
Ango Abdullahi ya ce duk da yadda birane a Arewa suka faɗaɗa, hakan ba yana nufin an samu ci gaba ba. A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙimomin da suka haɗa da gaskiya, biyayya ga doka, mutunta jama'a da shugabanci mai hidimar al'umma.
Ya ce idan Arewa ba ta rasa waɗannan ƙimomi ba, da ba ta tsinci kanta cikin matsalolin rashin tsaro, talauci da koma bayan ci gaba ba.
Bugaje ya soki shugabannin Arewa
Shi ma Farfesa Usman Bugaje ya bayyana cewa matsalolin Arewa sun ƙaru ne saboda shugabanni sun yi watsi da manufofin waɗanda suka kafa tubalin ci gaban yankin.

Kara karanta wannan
Ganduje ya tsokano NDC da Obidents, sun yi masa raddi mai zafi kan taba Obi, Kwankwaso
Ya ce noma ya durƙushe, talauci ya ƙaru, ilimi da lafiya sun tabarbare, yayin da rashin tsaro ke ci gaba da addabar al'umma.
The Nation ta ruwaito Bugaje ya ce abin takaici ne yadda wasu daga cikin manyan Arewa suka mayar da korafi kawai sana'a ba tare da gabatar da mafita ga matsalolin yankin ba.
Ya kuma tuna yadda marigayi Janar Hassan Katsina ya taɓa ƙarfafa shi ya ci gaba da rubuce-rubucen da ke kare muradun Arewa, duk da matsin lambar da ya fuskanta daga jami'an ƙasashen waje.

Source: Facebook
Kiran dawo da kyawawan dabi'un Arewa
Masu jawabin sun bayyana cewa shugabannin Hassan Katsina sun yi fice wajen gaskiya, tawali'u, biyayya ga ƙa'idoji da sadaukarwa ga al'umma.
Sun ce idan shugabannin yau suka rungumi irin waɗannan dabi'u, Arewa za ta iya shawo kan matsalolin da suka dabaibaye ta.
Sun bukaci shugabannin Arewa su daina fifita muradun kansu, su mayar da hankali wajen yi wa jama'a hidima, tare da tabbatar da adalci da gaskiya domin dawo da martabar yankin da bunƙasa rayuwar al'umma.
IBB ya fadi matsalar Arewa
A wani labari, mun ruwaito cewa, matsalar tsaro da karuwar talauci a Najeriya sun mamaye tattaunawa a Kaduna yayin da Ibrahim Badamasi Babangida ya ba da shawara.
IBB da Laftanar Janar Alani Akinrinade mai ritaya sun bayyana damuwa cewa kasar ta rasa shugabanni masu tarbiyya, kishin kasa da nagarta.
Dattawan sun gargadi cewa Arewa na ci gaba da shiga matsanancin halin tattalin arziki da zamantakewa saboda halayen shugabanci irin wanda Katsina ya yi ba sa fitowa a cikin ‘yan siyasar yau.
Asali: Legit.ng

