ADC Ta Gamu da Koma Baya, Na Kusa da El Rufai Ya Fice daga Jam'iyyar a Kaduna

ADC Ta Gamu da Koma Baya, Na Kusa da El Rufai Ya Fice daga Jam'iyyar a Kaduna

  • Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Mainan Zazzau, ya yi murabus daga ADC kwanaki kadan bayan jam’iyyar ta warware rikicin shugabancinta a Kaduna
  • Murabus din ya zo ne bayan Bello ya sha kaye a zaben fidda gwani na kujerar gwamnan Kaduna, inda Isa Ashiru ya samu tikitin jam’iyyar
  • Ficewar tasa na iya sake jawo tambayoyi kan hadin kan ADC a Kaduna, bayan jam’iyyar ta yi sulhu tsakanin bangarorinta masu adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kwanaki kadan bayan ADC ta sanar da matakan da ta dauka wajen warware rikicin shugabancinta a jihar Kaduna, wani jigo ya fice daga jam'iyyar.

Daya daga cikin ‘yan takararta na kujerar gwamna da suka sha kaye, Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Mainan Zazzau, ya yi murabus daga jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Peter Obi: An ji abin da ya faru da dan takarar NDC ya tattauna da jakadan Birtaniya

Mainan Zazzau ya raba gari da jam'iyyar ADC
Tsohon mai neman takarar gwamnan Kaduna a ADC, Muhammad Bello Hoto: Muhammad Sani Bello
Source: Facebook

Wasikar murabus din da Premium Times ta gani ta nuna cewa Muhammad Bello ya fice daga ADC a hukumance a ranar 21 ga Yuli.

Murabus din ya zama sabon koma baya ga jam’iyyar adawar, wadda a baya-bayan nan ta yi sulhu tsakanin bangarorinta masu adawa karkashin jagorancin dan takararta na zaben gwamna na 2027, Isa Ashiru, a wani yunkuri na karfafa damar da take da ita na kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.

Mainan Zazzau ya bar ADC

An aika wasikar ne ga shugaban jam’iyyar na mazabar Sabon Gari, kuma shugabannin mazabar sun karbe ta, rahoton tashar Channels tv ya nuna hakan.

Ko da yake Muhammad Sani Bello bai bayyana dalilin matakin nasa ba, ficewarsa ta zo ne watanni kadan bayan ya tsaya takarar tikitin gwamnan jam’iyyar, wanda Ashiru Kudan ya samu.

Tarihin sauya sheka

Muhammad Sani Bello ba bako ba ne wajen sauya gidan siyasa a jihar Kaduna. Ya dade yana tare da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, amma daga bisani ya sauya sheka ya goyi bayan Gwamna Uba Sani, wanda ya nada shi Kwamishinan Ilimi.

Kara karanta wannan

ADC: Ashiru Kudan ya zabi abokin takarar gwamna domin doke Uba Sani a Kaduna

Sai dai bayan ya shafe sama da shekara guda a majalisar zartarwar jihar, ya yi murabus daga gwamnatin Uba Sani.

Daga bisani ya koma gidan siyasar El-Rufai, sannan ya shiga ADC gabanin zaben 2027, inda ya nemi tikitin jam’iyyar na kujerar gwamna amma bai samu ba.

Mainan Zazzau ya fice daga jam'iyyar ADC
Mainan Zazzau, Alhaji Muhammad Bello Hoto: Prince Prince
Source: Facebook

Sababbin tambayoyi kan ADC

Ficewar Bello ta zo ne a wani lokaci mai muhimmanci ga ADC a Kaduna.

A wannan makon ne Ashiru ya sanar da cewa bangarorin da ke adawa da juna a jam’iyyar sun binne bambance-bambancensu bayan shafe watanni suna rikici, inda ya bayyana sulhun a matsayin wani muhimmin sauyi a shirye-shiryen jam’iyyar na zaben 2027.

Yanzu da daya daga cikin fitattun masu neman takarar kujerar gwamna ya fice daga jam’iyyar, murabus din na iya sake haifar da damuwa kan hadin kan ADC, duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma kwanan nan.

Iyalan El-Rufai sun nesanta kansu da wasika

A wani labarin kuma, kun ji cewa iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun nesanta kansu da wata wasika da ake cewa ya rubuta zuwa ga shugabannin ADC.

Iyalan El-Rufai sun ce makiya ne suka kirkiri takardar domin kulla makirci da haifar da rudani a jam’iyyar hamayya ta ADC a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng