Yadda Wani Dan Majalisar Wakilan Najeriya Ya Gagara Biyan Kudin Makarantar 'Yarsa
- Ɗan majalisa Chinedu Obika ya ce wani abokin aikinsa ya kasa tara N700,000 don biyan kuɗin makarantar ’yarsa watanni biyu da suka gabata
- Chinedu Obika ya bayyana cewa shi ne ya kai agajin gaggawa inda ya taimaka wa ɗan majalisar ya biya kuɗin makarantar
- Dan majalisar ya ce lamarin ya nuna cewa ba dukkan ’yan majalisar ne ke cin moriyar abin da ake kira “azurtar da kai” ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
FCT, Abuja - Ɗan majalisar wakilai, Chinedu Obika, ya bayyana cewa wani abokin aikinsa ya kasa tara N700,000 don biyan kuɗin makarantar ’yarsa watanni biyu da suka gabata,.
Dan majalisar ya bayyana cewa hakan ya sa shi da kansa ya taimaka masa wajen biyan kuɗin makarantar.

Source: Facebook
Ɗan majalisar ya yi wannan bayani ne a wata hira da shirin KAA Truths, wadda aka wallafa ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026.
Obika, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta AMAC/Bwari a Babban Birnin Tarayya (FCT), ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan ra’ayin jama’a cewa ’yan majalisa na karɓar albashi mai yawa.
Obika ya bayyana abin da ya faru
Obika ya ce lamarin ya nuna cewa ba dukkan ’yan majalisar ne ke amfana da abin da ’yan Najeriya ke dangantawa da Majalisar Ƙasa na “azurtar da kai” ba.
“Yanzu bari na gaya muku wani abu da ba ku sani ba. Zan iya gaya muku cewa kimanin watanni biyu da suka gabata, wani abokina ɗan majalisa ya kasa biyan N700,000 na kuɗin makarantar ’yarsa, kuma ni ne na taimaka masa wajen biyan kuɗin; ɗan majalisa fa!”
- Chinedu Obika
Ya ce lamarin ya tabbatar da cewa wasu ’yan majalisar da ke yin shiru a majalisa ba lallai ne hakan ya kasance saboda ana biyan su su yi shiru ba, domin wasu ba su da wani abin da za su nuna na amfanin da suka samu daga mukamansu.
“Saboda haka, idan batun azurtar da kai ne ya sa ’yan majalisa ba sa magana, to idan ba ka samun komai, ba za ka yi magana ba."
“Ban taɓa ganin irin wannan abu a rayuwata ba, a gaskiya ma, wani ɗan majalisa ya yi faɗa a kansa. ’Yan Majalisa suna faɗa idan abubuwa masu kyau suka zo musu, ba idan suka yi shiru ba. Don haka mutanen waje suna tunanin cewa idan sun yi shiru ne ake samun matsala,” in ji shi.
Bai bayyana sunan dan majalisar ba
Obika bai bayyana sunan ɗan majalisar da lamarin kuɗin makarantar ya shafa ba a yayin hirar da aka yi da shi.
Sai dai ya dage cewa duk wani haƙƙi ko alawus da ya kamata ɗan Majalisa ya samu, bayanai ne da jama’a za su iya gani, yana mai ƙalubalantar ’yan Najeriya da su nemi takamaiman bayanai maimakon dogaro da ikirarin da ba a tabbatar da su ba game da kuɗaɗen da ’yan majalisa ke samu.
“Duk wani haƙƙi da aka tanada wa ɗan majalisa yana nan a fili ga jama’a. Idan ba ka samu wani takamaiman abu ba, ka ce mini, ‘Mai girma, an ce wannan shi ne kaza da kaza’, kuma zan amsa maka kai tsaye.”
- Chinedu Obika

Source: Original
Sanata ya koma PDP daga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata Olubiyi Fadeyi da ke wakiltar mazabar Osun ta Tsakiya, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC shekara guda kacal bayan shiga jam'iyyar.
Fadeyi ya bayyana hakan ne cikin wasiƙar murabus da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take.
Asali: Legit.ng

