Gwamna Ya Maka EFCC a Kotu bayan Rufe Asusun Gwamnatinsa ana Shirin Zaɓe
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya shigar da ƙara kan hukumar yaki da cin hanci a Najeriya ta EFCC
- Gwamnatin Osun ta ce EFCC ba ta da ikon rufe asusun gwamnati ba tare da umarnin kotu ba
- Yayin da EFCC ta ce tana binciken zargin karkatar da Naira biliyan 11, Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar ta garzaya kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Osun - Gwamnan Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Hukumar EFCC.
Hakan ya biyo bayan hukumar yaki da cin hanci ta rufe da asusun rabon kuɗaɗen gwamnatin jihar.

Source: Instagram
A cikin ƙarar, Adeleke tare da Babban Lauyan Jihar da Akanta Janar sun nemi kotu ta ayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa doka da kundin tsarin mulki, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
An yi walƙiya: ADC ta nemi Tinubu ya yi wa El Rufa'i yadda aka yi wa gwamnatin Osun
Matakin EFCC na rufe asusun gwamnatin Osun
An sanya EFCC, shugaban hukumar da bankin First Bank a matsayin waɗanda ake ƙara, masu ƙarar sun ce EFCC ba ta da ikon sanya takunkumi ko umarni kan asusun gwamnatin jihar ba tare da samun ingantaccen umarnin kotu ba, kamar yadda kundin tsarin mulki da dokokin EFCC da dokar hana safarar kuɗi suka tanada.
Sun kuma roƙi kotu ta tantance ko umarnin da EFCC ta aika wa bankin a ranar 5 ga Agustan 2026 na daskarar da asusun gwamnatin Osun ya kasance bisa doka.
A cewarsu, matakin ya zama amfani da iko ba bisa ka'ida ba, tare da tauye ikon gwamnatin jihar da hana jama'a cin moriyar dimokuraɗiyya.

Source: Original
Bukatar masu karar EFCC kan rufe asusun
Masu ƙarar sun ce First Bank ma bai kamata ya aiwatar da umarnin EFCC ba tare da sahihin umarnin kotu ba, sun bayyana cewa matakin ya hana gwamnatin jihar gudanar da ayyukanta na kundin tsarin mulki, wanda zai iya shafar biyan ma'aikata da aiwatar da ayyukan gwamnati.
Saboda haka, sun roƙi kotu ta ayyana daskarar da asusun a matsayin haramtacciya kuma marar inganci.
Sun kuma nemi a soke duk wani takunkumi da aka sanya kan asusun tare da umartar bankin ya ba gwamnatin Osun damar ci gaba da amfani da asusun ba tare da wani cikas ba.
Baya ga haka, sun nemi kotu ta hana EFCC da jami'anta sake daskarar da kowane asusun gwamnatin Osun ba tare da bin tanadin doka ba.
Haka kuma sun buƙaci a hana First Bank bin duk wata wasiƙa ko umarni daga EFCC da ba ta samu amincewar kotu ba, cewar Punch.
Gwamnatin Osun ta kuma nemi kotu ta ba ta diyyar Naira biliyan biyu a matsayin tara da diyya saboda abin da ta kira tsoma baki ba bisa ƙa'ida ba cikin kuɗaɗen jama'a.
Har yanzu kotu ba ta sanya ranar sauraron ƙarar ba, an shigar da ita ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci EFCC da ta garzaya kotu domin a cire takunkumin da aka sanya wa asusun rabon kuɗaɗen gwamnatin Osun.
A ranar Laraba, EFCC ta tabbatar da cewa ita ce ta rufe asusun, tana mai cewa matakin yana da alaƙa da binciken zargin karkatar da kuɗaɗen Ecology Funds, Intervention Funds da kuɗaɗen FAAC da ya kai Naira biliyan 11.
Rufe asusun Osun: Tinubu ya umarci EFCC
An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar EFCC ta koma kotu domin janye umarnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun.
Tinubu ya ce lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba saboda zaɓen gwamnan Osun ya rage saura kwanaki kaɗan.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta 'yancin hukumomin bincike su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma baki ba.
Asali: Legit.ng

