Akwai Kura: Kamfanin da Atiku Ya Dauka Haya, Ya Kunno Sabuwar Wuta ga Tinubu a Amurka
- Kamfanin Von Batten mai alaƙa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sake neman a fitar da bayanan da suka shafi shari'ar Shugaba Bola Tinubu a Amurka
- Kamfanin ya ce zai gana da ƙungiyoyin yaƙi da miyagun ƙwayoyi, shugabannin addinai da waɗanda suka taɓa fuskantar matsalar shan tabar kwaya
- Ta zargi hukumomin Amurka da ƙin fitar da bayanan da suka shafi zargin alaƙar Tinubu da binciken safarar kwaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Kamfanin da Atiku Abubakar ya dauka haya, ya sake neman a fitar da bayanan da suka shafi shari'ar Shugaba Bola Tinubu a Amurka.
Kamfanin ya kuma sanar da shirin tattaunawa da ƙungiyoyin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da waɗanda suka fuskanci matsalar shan kwaya.

Source: Facebook
Kamfanin Von Batten-Montague-York ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, 25 ga watan Yulin 2926.
Ya zargi hukumomin tsaron Amurka a ƙarƙashin tsohon Shugaba Joe Biden da ƙin fitar da bayanan da suka shafi zargin alaƙar Tinubu da binciken safarar kwaya duk da buƙatun da aka gabatar a ƙarƙashin dokar 'yancin samun bayanai FOIA.
An nemi bayanan hukumar FBI kan Tinubu
A cewar kamfanin, mai fafutukar tabbatar da gaskiya a Amurka, Aaron Greenspan, ne ya gabatar da buƙatun ga Hukumar Binciken Tarayya (FBI), Ma'aikatar Shari'a da Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi (DEA).
Kamfanin ya jera lambobin buƙatun FOIA kamar haka: 1588244-000, 1593615-000, 22-00892-F, 24-00201-F da EOUSA-2023-002028
Sanarwar ta ce:
“FBI, Ma'aikatar Shari'a da DEA a ƙarƙashin Shugaba Joe Biden sun ƙi buƙatun FOIA na fitar da bayanan da suka shafi zargin safarar kwaya da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi daga Najeriya zuwa Chicago."
“Aaron Greenspan, wani ɗan Amurka mai fafutukar tabbatar da gaskiya, ne ya gabatar da buƙatun FOIA. Ƙin amincewa da buƙatun da kuma jan ƙafa da gwamnatin Biden ta yi ya sa Alƙalin Kotun Gundumar Amurka Beryl Howell ya umarci gwamnatin Biden a shekarar 2025 da ta fitar da bayanan. Sai dai har yanzu ba a fitar da wani fayil ba. Wannan zai canza.”
Za a gana da kungiyoyin yaƙi da miyagun kwayoyi
Kamfanin ya kuma sanar da shirin gana wa da ƙungiyoyin yaƙi da miyagun ƙwayoyi, shugabannin addinai da waɗanda suka fuskanci matsalar shan kwaya a Amurka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Kamar yadda Shugaba Donald Trump ya nuna da gaskiya, bai kamata hukumomin Amurka su taɓa kare shugabannin ƙasashen waje da ake zargi da alaƙa da miyagun ƙwayoyin da aka yi safararsu zuwa Amurka ba."
“Mako mai zuwa, za mu gana da ƙungiyoyin yaƙi da miyagun ƙwayoyi, shugabannin addinai da waɗanda suka fuskanci matsalar shan kwaya da mutuwar mutane da ta samo asali daga hakan, dangane da zargin alaƙar Shugaba Tinubu da safarar kwaya a Chicago.”

Source: Twitter
An yi hasashen nasarar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fasto dan Najeriya, Prophet Elijah Bamidele, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu gabanin zaben 2027.
Prophet Elijah Bamidele ya yi hasashen cewa shugaban kasar mai ci zai ci gaba da rike kujerar shugaban kasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng

